Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sanya hannu kan dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arziki ta Zamani (GITDEC), domin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaban tattalin arziƙin jihar.
Gwamnan ya ce kafa wannan hukuma wani muhimmin mataki ne da zai taimaka wajen sanya Gombe cikin jihohin da ke tafiya da zamani a ɓangaren fasaha.
“Ayyukan hukumar sun haɗa da samar da cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire, bunƙasa fasahar zamani, koyar da dabarun zamani, da kuma aiwatar da ayyukan gwamnati ta yanar gizo,” in ji gwamnan.
Haka kuma hukumar za ta tallafa wa matasa da masu ƙirƙira, ta samu hannun jari a fannin fasaha, da kuma tabbatar da tsaron bayanan gwamnati.
Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya miƙa kwafin dokar da aka amince da ita ga Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, Farfesa Abdullahi Bappah Garkuwa, domin fara aiwatarwa.
Farfesa Garkuwa, ya ce kafa hukumar babbar nasara ce ga ci gaban fasaha a jihar, kuma za ta kawo ayyukan yi ga matasa, mata, da ’yan kasuwa.
Wannan ci gaba na zuwa ne a lokacin da Gwamnatin Gombe ke ƙara haɗa kai da hukumomin fasaha na cikin gida da na ƙasashen waje, irin su NITDA da Uniccon Group, domin ƙara inganta kayan aikin fasaha da horaswa a jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link