Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba.
“Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa-kai domin kawo ƙarshen barazanar ta’addanci.”
A nasa jawabin, Rabiu Baushe, ya gode wa gwamnan bisa wannan tallafi, inda ya bayyana cewa motocin da baburan za su ƙara musu ƙarfi wajen yin sintiri da shawo kan hare-hare a yankunan karkara.
Ya kuma yi alƙawarin cewa ƙungiyar PROHAN za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a dukkanin sassan Jihar Gombe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link