Gwamnan Bauchi Ya Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Malami Sheikh Dahiru Usman

[ad_1]


Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya yi alhinin rasuwar babban malamin addinin Muslunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamba.

A saƙon ta’aziyya da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Mukhtar Gidado, Gwamnan a madadin iyalansa, gwamanti da al’ummar jihar Bauchi, ya nuna matuƙar jimamin wannan babban rashin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa marigayin, almajiransa, ɗalibai da ma al’ummar Musulmi a faɗin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, cike da baƙin ciki da jimami na rashi, gwamnatin jihar Bauchi ta na sanar da rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci, jagora, kuma babban shugaban addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya koma ga mahaliccinsa da sanyin safiyar yau Alhamis 27 ga watan Nuwamba 2025 a Bauchi yana da shekaru 102 a duniya.”

A cewar Gwamna Bala Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kasance jigo ne a fannin ilimin addinin Islama, mutum ne mai zurfin imani, kaskantar da kai, da hikima, tawali’u da sadaukar da kai domin addinin Musulunci, “Rayuwarsa ta duƙufa wajen yaɗa addinin Musulunci, karantar da Alƙur’ani mai girma, da kuma koyar da ɗabi’u da saita zukatan mutane bisa daidai.”

Ya ƙara da cewa ta hanyar kama Makarantu da daman gaske da cibiyoyin koyar da addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman ya ilmantar da dubban ɗalibai waɗanda suka haddadace Alƙur’ani mai girma da ilimin addinin Muslunci a fannoni daban daban a fadin Afrika.

Ya kuma nuna cewa irin salon koyarwar malamin na son zaman lafiya da ci gaban ƙasa hadi da neman haɗa kan jama’a ba za su misaltu ba, waɗanda za a ci gaba da tunawa da su tsawon shekaru.

Gwamna Bala Mohammed ya ce Babban rashi ne aka yi na jajirtaccen malami wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bauta wa Allah da hidimarta masa da koyarwa da bada tarbiyya wa jama’a, “Tarihin rayuwasa zai cigaba da wanzuwa har al’ummar da za su nan gaba su yi koyi.”

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Bauchi za ta ci gaba da karrama shi da bada gudunmawa wa Cibiyoyin da ya bari domin ci gaba da kyautata ilimin addinin Musulunci da ɗa’a da cigaban al’umma.

Ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa ya sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa iyalansa da almajiransa da al’ummar Musulmai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *