Fadar Shugaban Ƙasa Ta Soki Jami’iyyar ADC, Ta Ce Su Fuskanci Matsalolinsu

[ad_1]

Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci jam’iyyar ADC ta daina zargin Bola Ahmed Tinubu da APC. Ta ce jam’iyyar ce ta fi dacewa ta gyara rikicin cikin gidan da take fuskanta.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Temitope Ajayi, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a. Ya ce matsalolin ADC sun faru neel sakamakon gazawar shugabanninta wajen tafiyar da harkokinsu.

  • ADC Ta Nemi Shugaban INEC Ya Yi Murabus
  • 2027: Gwamnan Bauchi Na Shirin Komawa ADC, Bayan Kasa Shawo Kan Rikicin PDP

Ajayi ya jaddada cewa ba gwamnati ko APC suka kai jam’iyyar kotu ba. Ya ce da an yi kyakkyawan tsari da lura da al’amura, da an kauce wa wannan rikici.

Ya zargi shugabannin ADC da ƙin ɗaukar alhakin kura-kuransu. Ya ce suna zargin INEC da shugabanta da kuma gwamnatin tarayya ba tare da hujja ba.

Fadar shugaban ƙasa ta buƙaci ADC ta maida hankali wajen warware rikicin cikin gidanta. Ta ce jingina laifi ga wasu ba zai magance matsalolin da ke damun jam’iyyar ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *