EFCC ta kama mutum uku da ake zargi da haƙar zinare a Borno

[ad_1]



Jami’an Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC reshen jihar Borno a Maiduguri sun kama mutane uku da ake zargi da haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Hukumar EFCC ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 17 ga Maris, 2026, inda ta bayyana cewa an kama mutanen ne a garin Malam Jakwa, cikin ƙaramar hukumar Hawul, bayan samun sahihan bayanai kan ayyukansu.

An gano waɗanda ake zargin da suka haɗa da: Umar Muhammad da Modu Bamai Umar da Sani Samaila.

A cewar hukumar EFCC, zargin da ake yi musu na haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba yana haifar da rashin tsaro da lalata muhalli a jihar.

Sanarwar ta ce, “An kama waɗanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanai kan ayyukan haƙar zinare da suka aikata ba bisa ƙa’ida ba.”

Kayayyakin da aka samu daga gare su sun haɗa da: ƙaramin injin auna zinare da adadin zinare da aka haƙo.

EFCC ta ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike don ya zama izina ga wasu masu ƙudirin irin na su.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *