EFCC ta kama jarumar Kannywood kan wulaƙanta takardar Naira
[ad_1]
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta kama jarumar Kannywood Samha M Inuwa bisa cin mutuncin Naira.
Hukumar ta ce ta kama Samha ne bayan wani bidiyo da ta yi tana share majina da takardar Naira 1,000 ya karaɗe soshiyal midiya.
Dele Oyewale, mai magana da yawun EFCC na ƙasa, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai wannan Talatar a Abuja.
Kakakin ya ce jami’an hukumar reshen Jihar Kano ne suka cafke jarumar wadda a yanzu haka tana hannu.
Kazalika, Oyewale ya ce za a gurfanar da jarumar a gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link