Dole A Ɗauki Matakan Gaggawa Kan Matsalar Ilimi Da Arewa Ke Fuskanta – Inuwa
[ad_1]
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira da a ɗauki matakan gama gari don magance matsalar rashin daidaiton samun ingantaccen ilimi a Arewacin Nijeriya, yana mai gargaɗin cewa makomar yankin na cikin hatsari idan ba a ɗauki matakai masu tsauri ba.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da jawabi a matsayin Shugaban Taron Tunawa da Sir Ahmadu Bello Karo Na 12 Kan Jagoranci da Shugabanci Nagari, wanda aka gudanar a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa a ranar Talata.
- Tinubu Ya Gudanar Da Ayyukan Raya Kasa Da Dama A Arewa A 2025 —Abdul’aziz Abdul’aziz
- Kafa Kamfanin Sarrafa Gwal A Legas: Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Ƙalubalanci Tinubu
An yi wa lakcar taken “Daidaito Wajen Samar da Ingantaccen Ilimi a Arewa – Lokaci Ne Na Yin Aiki Da Gaske.”
Gwamnan ya bayyana taken a matsayin wanda ya dace kuma ya nuna tarihin rayuwar Marigayi Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, inda ya ce ilimi shi ne ginshiƙi mafi ƙarfi na samar da arziki, haɗin kai da ci gaba a Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
Kamar yadda Kakakinsa Isma’ila Uba Misilli ya naƙalto, ya tunatar da mahalarta taron cewa lakcar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan da ƙasar nan ta cika shekaru 60 da juyin mulkin farko da aka yi a ranar 15 ga watan Janairun 1966, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Sir Ahmadu Bello, da Firayim Minista Abubakar Tafawa Balewa da sauran shugabannin ƙasa.
A cewarsa, hanya mafi kyau ta tunawa da girmamasu ba kuka ba ce, sai dai ta yin aiki mai ma’ana wanda ya dogara kan shugabanci nagari da ci gaba mai damawa da kowa.
Gwamna Yahaya ya bayyana damuwa game da ƙididdigar ilimi mai ban tsoro a Arewa, yana mai cewa Nijeriya tana da yara fiye da miliyan 18 da ba sa zuwa makaranta, inda kusan kaso 70 cikin 100 na yaran suna Arewacin Nijeriya ne.
Ya ƙara da cewa adadin waɗanda suka iya karatu da rubutu a wasu jihohin Arewa bai kai kaso 30 cikin ɗari ba, yayin da ‘ya’ya mata masu zuwa makaranta da kuma yawan waɗanda suka iya karatu da lissafi har yanzu yake ƙasa sosai.
Gwamnan ya jaddada cewa dole ne ƙalubalen ilimi ya kasance a sahun gaba cikin ƙudurorin shugabannin Arewa.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin na Arewa ya bayyana cewa gwamnonin yankin su na ci gaba da fifita ilimi ta hanyar yin aiki tare da Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Ƙasa (UBEC), da abokan hulɗar ci gaba da kuma hukumomin bada gudummawa don faɗaɗa damammakin shiga makarantu, da inganta ababen more rayuwa da kuma ƙarfafa hazaƙar malamai.
Ya kuma ambaci kafa Asusun Tsaro na Arewacin Nijeriya a matsayin wani muhimmin mataki na magance matsalolin tsaro, wadda ya bayyana a matsayin babbar barazana ga ilimi a yankin.
Ya bayyana cewa, an tsara asusun ne don samar da kuɗaɗen tallafi mai ɗorewa da nufin kyautata harkokin tsaro don kare makarantu.
Ƙungiyar, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, sun ƙaddamar da shirye-shirye kamar Taron Ilimi na Nijeriya na 2025 da kuma tarurrukan bita a matakan jihohi kan ilimi daga tushe don inganta harkokin karatu da lissafi na yara a matakin farko da kuma mayar da miliyoyin yara zuwa aji.
Da ya koma kan Jihar Gombe, Gwamnan ya bayyana manyan gyare-gyaren da gwamnatinsa ta yi, ciki har da ayyana dokar ta-vaci kan ilimi, da kafa wani babban kwamitin aiki da cikawa don farfaɗo da ilimi daga tushe, da kuma ƙaddamar da tallafin Naira biliyan 13 da miliyan 500 don inganta makarantun sakandare 442.
Ya ƙara da cewa Jihar Gombe ta ɗauke yara kimanin 450,000 da ba sa zuwa makaranta zuwa azuzuwa tsakanin 2019 zuwa 2025, ta kuma faɗaɗa damammakin shiga manyan makarantu tare da samar da sabbin rassan jami’o’i, da sake gina makarantun masu buƙata ta musamman, da tallafin karatu da ake bai wa ‘yan asalin jihar da kuma biyan kuɗaɗen jarrabawa ga ɗaliban makarantun sakandare.
Ya yaba wa Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello saboda ci gaba da shirya irin waɗannan lakcoci a kowace shekara.
Ya yi amfani da wannar damar wajen sanar da muhimman gyare-gyare a cikin ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa, ciki har da kafa wata babbar sakatariya ƙarƙashin jagorancin babban darakta, Mista Ezekiel Gomos, don inganta haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ‘yan Arewa kan batutuwan ci gaba.
[ad_2]
Source link