Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike

[ad_1]



Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare.

Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar.

Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor.

Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata.

Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya zama dole, domin idan ba a yi shi ba, babu wanda zai shugabanci matakin ƙananan hukumomi bayan ka8rewar dokar ta-ɓaci.

Wike ya ce: “Ranar 18 ga watan Satumba dokar ta-ɓaci za ta ƙare, kuma gwamna da ’yan majalisa za su koma bakin aikinsu.

“Kotun Ƙoli ta soke zaɓen da ya gabata, don haka idan ba a gudanar da wannan zaɓen ba, hakan na nufin babu shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.”

Ya kuma ƙara da cewa kayan zaɓe sun isa a kan lokaci, kuma jama’a suna kada ƙuri’arsu cikin kwanciyar hankali.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *