Farashin Kayayyaki A Nijeriya Sun Sauka Zuwa Kashi 21.88%
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin…