Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13
Majalisar Dokokin Jihar Gombe, ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomin ci gaban Ƙananan Hukumomi 13 da Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar. Ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu cikin rana guda. Kakakin majalisar, Abubakar Muhammad Luggerewo, ya bayyana hakan ne yayin zaman sauraron ra’ayin jama’a a kan ƙudirin, wanda…