Category: Latest News

  • El-Rufai da Ribaɗu na cacar baka kan biyan ’yan bindiga kuɗaɗen fansa

    [ad_1]



    Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace.

    El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ta ƙara ƙamari, duk da cewa gwamnati ta yi ƙoƙarin rage yadda ake rahoto a kafafen watsa labarai.

    Har yanzu ina kan bakata cewa waɗannan ’yan bindiga a halaka su baki ɗaya, ba a rika lallashi ko yin sulhu da masu ta’addanci ba. Wannan bai taba aiki a ko’ina ba,” in ji shi a yayin tattaunawar.

    Martanin ONSA

    A martanin da aka fitar da safiyar Litinin, Ribadu ya bayyana zargin na El-Rufai a matsayin “karya kuma mara tushe.”

    Ya ƙara da cewa babu wani lokaci da ofishinsa (ONSA) ko wani ɓangare na gwamnatin Tinubu suka taɓa biyan kuɗaɗen fansa ko bayar da wani irin tallafi ga masu aikata laifuka.

    A cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Shari’a na ONSA, Zakari Mijinyawa, ya sanya hannu a madadin Ribadu, an ce, “Wannan iƙirarin ba shi da tushe. A kowane lokaci ONSA na kira ga ’yan Najeriya da su guji biyan kuɗaɗen fansa. Waɗannan zarge-zargen sun saɓa da hujjojin da ake da su a ƙasa.”

    Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki dabara mai kaifi biyu wajen yaki da ’yan ta’adda — amfani da ƙarfin soja da kuma tattaunawa da al’umma don shawo kan ƙorafe-ƙorafen cikin gida.

    Matsalar ysaro a Arewa

    Najeriya na fuskantar ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga, waɗanda kan sace mutane don neman kuɗaɗen fansa, su kashe ko su ƙone ƙauyuka, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

    A cewar cibiyar nazari ta SBM Intelligence da ke Legas, sama da mutane 4,000 aka yi garkuwa da su a 2023 kacal, inda biya kuɗaɗen fansa na biliyoyin Naira.

    Haka kuma ƙasar na fama da matsalar Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, wanda ke ƙara dagula lamarin tsaro.

    Ribadu ya kare nsarorin sojoji

    Ribaɗu ya ce sojoji da jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara a wasu sassan Jihar Kaduna, ciki har da Igabi, Birnin Gwari da Giwa, inda aka kashe ko kama wasu daga cikin manyan shugabannin ’yan bindiga.

    “A Kaduna kaɗai, an halaka manyan kwamandoji kamar Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari da Boka. Haka kuma an kama jagororin Ansaru da suka kafa sansanoni a jihar, inda wasu daga cikin jaruman sojojimmu sun rasa rayukansu,” in ji Ribadu.

    Ya ce ikirarin El-Rufai na cewa gwamnati na biyan kuɗaɗen fansa bai dace da irin waɗannan sadaukarwa da aka yi ba.

    Siyasa ko tsaro?

    Wasu masu sharhi sun bayyana cacar bakan tsakanin Ribaɗu da El-Rufai a matsayin wani sabon babi na rikicin siyasa tsakanin tsofaffin abokan hulɗa.

    El-Rufai, wanda ya yi wa Tinubu kamfe a zaben 2023, ya daɗe yana sukar gwamnatin, musamman a fannin tattalin arziki da tsaro, yana mai cewa ba ta taka rawar da ake sa ran za ta taka ba.

    Ribadu, wanda tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ne, ya yi kira da a guji sanya siyasa cikin al’amuran tsaro, yana mai cewa, “Yaƙi da ’yan ta’adda yaƙi ne na kowa, ba wurin yin siyasa ba ne. Duk wanda ke da matsala ya kamata ya bayar da shawara maimakon yaɗa bayanan ƙarya.”

    Me da ke tafe?

    Tsaron Najeriya ya kasance babban kalubale ga gwamnatin Tinubu tun hawansa mulki a watan Mayun 2023.

    Duk da rahotannin cewa wasu wurare sun samu natsuwa, har yanzu ana kai hare-hare a kauyuƙa, inda ba a samun isassun jami’an tsaro.

    Ƙungiyoyin farar hula sun buƙaci gwamnatin ta ƙara saka jari a fannin tsaro, ta ƙara ɗaukar sojoji da ’yan sanda tare da samar musu isasshen horo da kayan aiki na zamani.

    Masana kuma sun ja hankalin cewa biyan kuɗaɗen fansa yakan ƙarfafa gwiwar ’yan bindiga wajen ci gaba da sace mutane.


    [ad_2]

    Source link

  • Gwamnan Neja Ya Kori Kwamishinoninsa Gaba Ɗaya

    [ad_1]

    Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sallami dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar.

    Gwamnan ya bayyana labari sallamar ta su ne a taron majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, da safiyar yau Litinin 1 ga Satumbar 2025

    Ya gode wa mambobin majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a duk inda makomar aiki ta kai su.

    Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa ya bar Sakataren Gwamnatin Jihar, da Shugaban Ma’aikatansa da kuma Mataimakinsa da wasu manyan jami’an ofishinsa a muƙamansu.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Sakkwata sun yi zanga-zanga kan kashe mutane 5 da sace Hakimi da limamai

    [ad_1]



    ’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu.

    Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Neja.

    A yayin zanga-zangar a ranar Lahadi, wani daga ƙauyen Rinaye ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro gare mu a ɗauki matakin korar mana ’yan bindigar su bar yankinmu.

    “Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace mana mutane kuma babu wasu jami’an tsaro da aka kawo mana don kare mu.”

    Ya ce ’yan bindigar sun tashi ƙauyuka uku a ranar Juma’a, sun tafi na biyu dana uku a ranar Assabar da Lahadi.

    “A garin Rinaye sun sace mai garinmu da duka limaman garin bayan sun kashe mutum uku sun yi garkuwa da wasu mutanen garin da ba a tantance yawansu ba, a wannan Asabar da Lahadi.

    “Shekaranjiya sun shiga garin Aske dodo da Tungar Barkenda Jandutse duk waɗannan wurare babu mutane a cikinsu yanzu, sun kashe mutane biyu da yin garkuwa da wasu 15,” a cewar majiyar.

    Ya ce hukumomin tsaro da gwamnati ba a abin da suka yi a yanzu, ko jaje ba a kai musu ba.

    Malama Tunba mai yara biyar mata uku da maza biyu daga ƙauyen Jandutse ta ce yanzu haka ba ta san inda ’ya’yanta suke ba tun da suka gudu a ranar Assabar, a haka ta yini ba abin da ta sa a bakinta.

    Tumba ta yi kira ga gwamnati ta taimaka musu da tsaro mu zauna a gidajensu cikin rufin asiri, wahalar da suke ciki ta yi yawa.

    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta jiha SEMA sun ce sun san da zaman ’yan gudun hijirar da suka gudu kan matsalar ’yan bindiga.

    Bayanin ya ce, “A Ƙaramar hukumar Shagari ɗaruruwan mutane sun bar muhallansu kan rashin tsaron da ya kunno kai a yankin suna neman ɗauki.

    “Don ganin halin da ake ciki, hukumomin sun tafi rukunin gidaje 30 a ƙaramar hukumar inda mutanen suka zauna sun tuntubi hakiman mutanen daga cikinsu akwai Hakimin ‘Yan Dundaji, Malam Muhammad Bello Magaji, da Maigarin Tungar-Barke, Muhammadu Tudu, wanda ya tabbatar da harin da aka kai musu kwana uku baya, yana da ’yan gudun hijira da yawa.

    Sauran ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Tungar-Barke, Lungu, Aske-Dodo, Tungar-Doruwa, Zango, ‘Yan Yandu, Tungar Na’anza, Ila, da sauransu.
    A halin da ake ciki hukumomin na kira ga gwammati ta kawo ɗaukin gaggawa musamman samar da tsaro a ƙauyukan don mutanen su koma gidajensu cikin aminci.

    Wakilinmu ya tuntubi shugaban karamar hukumar Shagari Honarabul Alhaji Maidawa sai dai bai samu jin ta bakinsa ba har zuwa haɗa labarin.


    [ad_2]

    Source link

  • Ƴansanda Sun Gano Motocin Sata 2 A Adamawa

    [ad_1]

    Rundunar Ƴansandan jihar Adamawa ta bayyana cewa jami’anta sun gano motoci biyu da aka sace, tare da kama wani mutum mai suna Musa Suleh da ake zargi da satar.

    Mai magana da yawun rundunar a jihar, SP Suleiman Yahaya, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon bayanan sirri da DPO na Yola Division ya samu, wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin a Jambutu Motor Park da ke ƙaramar hukumar Yola ta Arewa.

    A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa cewa ya saci wata mota ƙirar Toyota Starlet mai lambar YLA-420 mallakar wani Babawo Abubakar na Ngurore, Yola ta Kudu. Haka kuma an gano wata mota ƙirar Toyota Starlet mai launin kore mai lambar JAL-861 CL a hannunsa, wadda bai gabatar da takardu ko hujjar mallaka ba.

    Kwamishinan Ƴansanda na jihar, CP Dankombo Morris, ya bayar da umarnin a miƙa shari’ar ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike da gano asalin motocin. Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa ba da bayanai cikin lokaci kan duk wani motsi da ya saɓa al’ada a unguwanninsu, tare da tabbatar da ƙudirin ta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

    Rundunar ta ce bayan kammala bincike, ana sa ran gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama Da Mutune 600 A Afghanistan

    [ad_1]

    Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa da ta afku a gabashin ƙasar ya haura mutane 610, yayin da aka samu ƙarin mutane 12 da suka mutu a Nangarhar, abin da ya kai jimillar mutuwar zuwa 622.

    Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka jikkata a lamarin. Rahotanni sun nuna cewa asibitoci da dama, musamman na lardin Asadabad, sun cika da marasa lafiya. Shugaban asibitin, Dr Muladad, ya bayyana cewa suna karɓar marasa lafiya daga girgizar ƙasar “a duk bayan minti biyar,” kuma mutane 188 cikin sa’o’i kaɗan aka kawo asibitin, ciki har da mata da yara.

    Sai dai hukumomi sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar yawan mutanen da suka mutu zai ƙaru, kasancewar yankin da abin ya shafa mai nisa ne, kuma ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa na fuskantar cikas wajen isa wurin.

    Girgizar ƙasar ta auku ne da dare lokacin da mutane suke barci a gidajensu. Rahotanni sun nuna cewa daruruwan mutane na iya kasancewa sun maƙale ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe, lamarin da ke ƙara tsananta fargaba da damuwa a yankin.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Isak Na Dab Da Zama Ɗan Wasa Mafi Tsada A Tarihin Firimiya

    [ad_1]

    Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala sanarwar a hukumance da misalin ƙarfe 7 na yamma.

    A farkon tattaunawar, Newcastle ta dage cewa sai Liverpool ta biya fam miliyan 130 kafin ta sayar da ɗan wasan, amma daga bisani aka amince da fam miliyan 125. Wannan mataki ya biyo bayan kwantiragin shekaru shida da Isak ya amince da shi a baya, inda ya nuna sha’awarsa ta komawa ƙungiyar mai horaswa Arne Slot.

    Tun lokacin bazara Liverpool ta fara zawarcin Isak, inda ta fara da tayin fam miliyan 110 da Newcastle ta ƙi amincewa da shi. Bayan tattaunawa mai tsawo, ƙungiyar ta cimma nasarar da take nema, yayin da Newcastle ta yanke shawarar siyar da ɗan wasan don buɗe hanya ga ɗaukar matashin ɗan wasan Jamus, Nick Woltemade.

    A cewar rahotanni, Liverpool za ta miƙa riga mai lamba 9 ga Isak, wanda hakan zai ƙara ɗaukaka matsayin sa a ƙungiyar. Idan aka kammala yarjejeniyar, zai kafa tarihi a matsayin ɗan wasan da aka fi kashe kuɗi akansa a gasar Firimiya, alamu kuma sun nuna cewa sanarwa a hukumance daga kungiyar na nan tafe.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Kwana 70 da ƙaddamar da taraktoci 2,000 na gwamnati har yanzu manoma ba su ga komai ba

    [ad_1]



    Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana.

    Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba.

    Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.”

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas (NEGF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafin kayayyakin noman damina da na rani.

    Taron ƙungiyar da ya gudana a Jalingo, Jihar Taraba a ƙarshen makon jiya, ya bayyana cewa tsadar kayayyakin noma da matsalar jinƙai na ƙara tsananta barazanar ƙarancin abinci.

    Gwamnonin sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafin noman rani tare da tabbatar da kayan aikin sun isa ga manoma ba tare da jinkiri ba.

    Yadda aka ƙaddamar da kayan aikin noman

    A ranar 24 ga watan Yuni, 2025, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin injinan noma a ƙarƙashin Shirin Fata Sabon Gobe, inda aka kawo taraktoci 2,000 daga ƙasar Belarus tare da kayan gyara, injinan girbi da sauransu.

    Gwamnati ta ce za a yi amfani da taraktocin wajen noma hekta 550,000 da samar da ayyukan yi 16,000 da kuma taimaka wa iyalan manoma fiye da dubu 550.

    Sai dai bincikenmu ya gano cewa har yanzu taraktocin suna an a ajiye a Cibiyar Hukumar Inganta Irin Noma ta Kasa (NASC) da ke Abuja.


    Manoma na ƙorafi

    Shugaban Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim, ya ce: “Abin mamaki ne har yanzu ba a raba taraktocin ba. Muna riƙon gwamnati ta hanzarta raba su ta hanyar da ta dace domin kada daminar bana ta wuce.”

    Haka ma Dakta Ogbo Douglas, shugaban Kungiyar Manoma Maso Rajin Ci-gaban (AFPA), ya bayyana jinkirin a matsayin “abin takaici.”

    Izinin Fadar Shugaban Ƙasa muke jira — Minista

    Wasu manyan jami’an Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya sun shaida wa Wakilinmu cewa an gama tsara yadda za a raba taraktocin jiha-jiha, amma ana jiran sahalewar Fadar Shugaban Ƙasa.

    Ministan Aikin Gona, Sanata Abubakar Kyari, ya ce, “Za mu tabbatar da cewa taraktocin za su yi aiki sosai ba wai a ajiye kawai ba. Da zarar mun samu izini, za mu fitar da tsarin farashin da zai zama mai sauƙi ga manoma,” in ji shi.

    A baya ma an sha yi wa manoma irin wannan alƙawarin amma ba tare da an cika ba.

    A 2018, an yi alƙawarin kawo taraktoci 10,000 daga kamfanin John Deere, sannan a 2021 aka ce za a kawo taraktoci 60,000, amma ba a aiwatar ba.


    [ad_2]

    Source link

  • Rashin Amincewa Da Tsarin Ƴan Kudancin Kaduna Ya Sa Suka Yi Min Mummunar Fassara

    [ad_1]

    Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kare salon mulkinsa na tsawon shekaru takwas da ya yi a jihar, inda ya jaddada cewa ya tabbatar da adalci da daidaito tsakanin kowane ɓangare, tare da ƙin amincewa da abin da ya kira “haƙƙoƙin mu ne” daga mutanen Kudancin Kaduna.

    Da yake jawabi a shirin ‘Social siyasa‘ na tashar talabijin ta Channels, El-Rufai ya ƙaryata zargin nuna son addini, yana mai cewa manufofinsa sun shafi kowa, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

    Ya bayyana cewa wasu mutane daga Kudancin Kaduna sun saba samun fifiko a ƙarƙashin gwamnatocin da suka gabata, wanda shi ya dakatar da shi da gangan, kana ya zargi wasu shugabannin Kirista daga yankin suna cin moriyar wasu tallafin kuɗi da gwamnatinsa ta daina bayarwa.

    Game da batun wakilci a gwamnati, El-Rufai ya musanta iƙirarin wariya, yana mai cewa naɗe-naden muƙaman gwamnati an riƙa yin su bisa daidaito tsakanin kowace mazabar sanata, ba wai bisa addini ko ƙabilanci ba.

    Kan batun goyon bayansa ga tikitin musulmi-musulmi na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, El-Rufai ya ce tsantsar dabarar siyasa ce kawai, kuma duk wani ɗan siyasa yana tafiya da lissafin yadda zai kai ga samun nasarar ne.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • NAJERIYA A YAU: Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara?

    [ad_1]

    Karin fannoni



    Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.

    Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa?

    Amsar wannan tambaya shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi yunkurin bicikowa.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link

  • Girgizar ƙasa ta kashe mutum 610 a Afghanistan

    [ad_1]



    Aƙalla mutum 610 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 1,300 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta afku a ƙasar Afghanistan.

    Rahotanni daga hukumomi da kafafen watsa labarai na duniya sun ce ibtila’in ya auku ne a yankin gabashin ƙasar Afghanistan, kusa da iyakarta da Pakistan.

    Rahoton Hukumar Binciken Ƙasa ta Amurka (USGS) ya bayyana cewa ƙarfin girgizar ƙasar ta kai matakin 6.0, kuma cibiyar ta kasance a wani yanki mai tazarar kilomita 27 daga birnin Jalalabad, inda ake da yawan jama’a kimanin 300,000.

    An gano cewa girgizar ta afku a zurfin kilomita takwas kacal daga saman ƙasa, wanda hakan kan ƙara tsananta illarta.

    Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya rawaito cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu zai ƙaru yayin da ake ci gaba da binciko gawarwaki da kuma ceton waɗanda ke cikin ɓaraguzan gine-gine.

    Haka zalika, New York Times ta ce an ji girgizar a Kabul — babban birnin Afghanistan — da ke tazarar kilomita 160 daga Jalalabad, duk da cewa ba a tabbatar da samun mace-mace a can ba.

    Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya wallafa a shafinsa na X cewa, “Muna cikin alhini kan asarar rayuka da asarar dukiya da wannan girgizar ƙasa ta haddasa a wasu yankunan gabashin ƙasarmu. Jami’ai da mazauna yankin suna ci gaba da aikin ceto.”

    Me ke kawo yawon girgizar ƙasa a Afghanistan?

    Afghanistan na fuskantar yawan girgizar ƙasa saboda matsayinta na tectonic.

    Wannan yanayi ne da ke haifar da fashewar ƙasa akai-akai, musamman a yankunan tsaunuka da ke gabashin ƙasar.


    [ad_2]

    Source link