Category: Latest News

  • Gwamnatin Tarayya Na Shiri Da Ƴan Bindiga, Tana Ba Su Biliyoyi — El-Rufai

    [ad_1]

    Tsohon gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Malam Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin tarayya da zaɓar hanya biyan kuɗaɗe da samar da kayan tallafi ga ƴan bindiga ƙarƙashin abin da ake kira dabarar “non-kinetic” wajen yaƙi da rashin tsaro. Ya bayyana cewa wannan tsari ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro (ONSA) ne ke jagoranta, tare da jaddada cewa akwai hujjojin tabbatar da hakan.

    A yayin tattaunawa a shirin Sunday Politics na gidan talabijin ɗin ChannesEl-Rufai ya bayyana cewa gwamnati na bai wa ƴan bindiga kuɗi da kayan abinci, lamarin da ya kira “tallafa wa ta’addanci”. Ya ce ba zai taɓa amincewa da irin wannan dabarar ba. “Abin da ba zan taɓa yi ba shi ne in biya ƴan bindiga, in riƙa ba su tallafi na kudi da abinci da sunan hanyar magance ta’addan ba da ƙarfin Soji ba. Wannan wauta ce. Tamkar muna ƙarfafar su ne,” a ji shi.

    El-Rufai ya jaddada cewa wannan tsari ba ya fitowa daga gwamnatin Kaduna kai tsaye, sai dai daga Abuja. A cewarsa, “Ba gwamnatin Kaduna ba ce, manufar gwamnatin ƙasa ce da ONSA yasa gaba, kuma Kaduna na ciki. Jihohi da dama sun nuna rashin amincewa, amma wannan ce manufar yanzu — rungumar ƴan bindiga. “

    Tsohon gwamnan, wanda ya daɗe yana fafutukar a yi amfani da ƙarfin Soji wajen murƙushe ƴan ta’adda, ya sake jaddada matsayinsa cewa “duk wani tubabben ɗan bindiga shi ne wanda aka kashe. Mu kashe su, mu buga da su, mu kawar da su baki ɗaya, sannan idan akwai kashi biyar cikin ɗari da suke son gyara, sai a taimaka musu. Ba za ka taba yin sulhu da maƙiya daga fuskar rauni ko tsoronsa ba, kuma ba za ka ba su kuɗi su je su sayi muggan makamai ba.”

    Ya kuma yi gargaɗi cewa muddin wannan manufar biyan kuɗaɗen da neman sulhu da ƴan bindiga na ci gaba, matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya ba za ta gushe ba. El-Rufai ya kuma zargi gwamnatin Kaduna ta yanzu da gazawa wajen kare al’umma, yana mai cewa an riƙa biyan kuɗaɗen fansa masu yawan gaske a asirce. “Ni na yi gwamna shekaru takwas, makarantu uku kacal aka kai wa hari. Wannan gwamnati ta shafe shekaru biyu amma fiye da hakan aka kai wa hari. An biya biliyoyin Naira a matsayin kuɗin fansa. Idan gwamnati ko kowa zai musanta, muna da hujjoji, kuma zamu bayyana su lokacin da ya dace,”in ji shi.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Shugabar Ma’aikatan Abuja ta rasu

    [ad_1]



    Allah Ya yi wa Shugabar Ma’aikata ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, Misis Grace Adayilo, rasuwa a safiyar Litinin ɗin nan.

    Shaidu sun tabbatar wa wakilinmu cewa ta rasu ne ’yan sa’o’i kaɗan da suka gabata. Kodayake kawo yanzu ba a sanar da rasuwar a hukumance ba.

    Misis Grace Adayilo ita ce mace ta farko kuma ’yar asalin yankin Babban Birnin Tarayya ta farko da ta riƙe wannan muƙami.

    ta kasance tsohuwar Sakatariyar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Birnin Abuja (AMAC), kafin Minista Nyesom Wike, ya naɗa ta Shugabar Ma’aikata.

    Ita ce ta wakilci Wike a babban taron Majalisar Taro ta Ƙungiyar G-7 da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata a Abuja.

    Ko a ranar Lahadi ta samu halartar ibada a coci, inda washegari aka samu labarin safiyar Litini.


    [ad_2]

    Source link

  • Ya kamata shugabannin Arewa su sa baki

    [ad_1]



    Ƙungiyar Arewa ta ’Yan Jarida (ABMPF) ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara, tana mai cewa matakin ya jawo asarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

    Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce rusau ɗin ya haddasa wa ’yan kasuwar asarar kimanin Naira biliyan 20, tare da ruguza shaguna da wuraren ibada fiye da 40, abin da ya ce “bai dace ba kuma yana iya jawo rikicin ƙabilanci.”

    Kungiyar ta roƙi gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da sarakuna na gargajiya su shiga wajen tabbatar da kare haƙƙin ’yan Arewa da suke zaune a Legas.

    Haka kuma ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sake duba matakin, ya samar da diyya da shirin sake mazauna kasuwar.

    Sai dai Gwamnatin Jihar Legas ta kare kanta, tana mai cewa aikin na daga cikin shirin gyaran birni da ake aiwatarwa domin ƙara inganta tsaro da tsarin kasuwanni.

    “Ba a yi wannan rushewar saboda ƙabila ko addini ba,” in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Tsara Birane ta jihar.

    “Mun fara gyara wuraren da ba su dace ba don samar da sabuwar kasuwa mai tsari da aminci ga kowa.”

    Gwamnatin ta ce tana nazarin matakan diyya da wurin da za a koma ga ’yan kasuwar da abin ya shafa, kodayake ba ta fitar da cikakken shiri ba tukuna.

    Amma ABMPF ta yi watsi da bayanin gwamnatin, tana mai cewa ba a bi ƙa’ida wajen aiwatar da rusau ɗin ba, sannan ba a bai wa ’yan kasuwa isasshen lokaci ko inda za su koma ba.

    “Abin takaici ne a kira al’ummar Arewa mazauna Alaba na tsawon shekara 80 da ’yan fiye da haka ’yan haya ko masu zama na wucin gadi da za a iya koran su duk lokacin da aka so,” in ji ƙungiyar.

    Ta ƙara da cewa matakin yana nuna yunƙurin kawar da ’yan Arewa da ’yan yankin Gabas daga Legas, abin da zai iya haifar da rikice-rikice a wasu jihohin Arewa inda Yarbawa ke zaune cikin lumana.

    Tasirin tattalin arziki

    Kasuwar Alaba Rago, wadda ta mamaye sama da hekta 10, wadda ta kasance cibiyar kasuwanci ga ’yan Arewa tun kafin samun ’yancin kai, ta tara dillalan dabbobi, hatsi da kayan gona da ake kawo su daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

    Masana tattalin arziki na gargaɗin cewa ruguza kasuwar zai iya shafar harkokin kasuwanci, kawo hauhawar farashi da rage harajin da jihar take samu daga irin waɗannan kasuwanni.


    [ad_2]

    Source link

  • NASFAT ta yi gargaɗi kan yin ɓatanci ga Sahabban Annabi (SAW)

    [ad_1]



    Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini.

    Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai a Jihar Kwara da wasu sassan Yammacin Najeriya sun shiga ce-ce-ku-ce saboda irin waɗannan kalamai a jan sahabban Annabi (RA).

    NASFAT ta ce addinin Musulunci ya umarci a yi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW) tare da girmamawa da ƙaunar sahabbai baki ɗaya.

    Sanarwar da kakakin NASFAT, Alhaji Shamsideen Owolabi Oseni, ya fitar ta ce,“Sahabbai ne suka fara yaɗa addinin Musulunci, suka kare shi, suka adana Alƙur’ani da Sunnah, sannan suka watsa shi ga al’ummomin da suka zo bayan su.”

    Ƙungiyar ta bayyana cewa yin batanci, ƙyama ko zagin sahabbai babban zunubi ne da malamai suka bayyana tun fil azal a matsayin alamar taɓewa, wanda masu aikatawa suna iya shiga kafirci.

    Ta ambaci manyan malaman Musulunci kamar Imam Ahmad, Imam al-Ɗahhaawi, Abu Zar’ah al-Raazi da Ibn Taymiyyah a cikin waɗanda suka yi gargaɗi cewa irin yin ɓatanci ga Sahabbai na girgiza tushen addinin Musulunci.

    NASFAT ta ƙara da cewa ƙaunar sahabbai alama ce ta imani, yayin da ƙin su ke nuna munafunci ko kafirci. Ta ce Allah Ya yaba musu a cikin Alƙur’ani kuma Ya nuna yardarsa da su.

    Kungiyar ta buƙaci malamai su kiyaye minbarorinsu daga kalaman rarrabuwar kawuna, tare da jaddada koyarwar da za ta ƙarfafa haɗin kai da gina al’umma ta fuskar addini da rayuwar yau da kullum.


    [ad_2]

    Source link

  • Yadda aka yi jana’izar ’yar Sarkin Katsina

    [ad_1]



    ’Yar Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Khadijah, wadda aka fi sani da Andijo, ta rasu.

    Ta rasu a Abuja tana da shekara 35, kuma ta bar ’ya’ya uku.

    An yi jana’izarta a fadar Sarkin Katsina ƙarƙashin jagorancin Imam Mustapha Gambo.

    Ɗaruruwan mutane sun halarci jana’izar, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da kuma al’ummar gari.

    Bayan kammala jana’izar, Gwamna Radda ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai tausayi kuma mai son zaman lafiya.

    Ya roƙi Allah Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa iyalanta haƙurin wannan rashi.

    Haka kuma, Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya raya ’ya’yanta uku da ta bari.

    Daga cikin manyan baƙi da suka halarci jana’izar akwai Mataimakin Gwamnan Katsina, Hon. Faruk Jobe; attajiri Alhaji Dahiru Mangal; Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Bello Shehu; Daraktan DSS, Jabiru Tsauri.

    Sauran sun haɗa da Lamidon Katsina, Alhaji Usman Abba Jaye; Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman; Dan Malikin Katsina; da kuma Wazirin Katsina, Alhaji Ida, da sauransu.


    [ad_2]

    Source link

  • Xi Jinping Ya Gana da naredra Modi

    [ad_1]

    A tsakar ranar yau Lahadi 31 ga wata, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Firayim ministan Indiya Narendra Modi wanda ya zo Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin kan Shanghai (SCO) na shekarar 2025 a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin.

    Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata shugabannin biyu sun sami nasarar yin ganawa a birnin Kazan, dangantakar Sin da Indiya ta sake farawa kuma ta ci gaba da samun ci gaba mai kyau. A bana an cika shekarun 75 da kafa huldar diflomasiyya tsakaninsu. Ya kamata bangarorin biyu su hange nesa kan raya dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare, kuma kara habaka dangantakarsu mai dorewa yadda ya kamata ta hanyar ganawar Tianjin. Matakan da suka dace wajen karfafa dangantakar sun hada da, da farko, ya kamata a kara tuntubar juna bisa manyan tsare-tsare, da kuma habaka amincewar juna. Na biyu, ya kamata a fadada huldar hadin gwiwa don cin moriyar juna. Na uku, kula da damuwar juna, da kuma nacewa kan yin zaman tare cikin lumana. Na hudu, ya kamata a karfafa hadin gwiwa tsakanin mabambantan bangarori don kare muradun gama gari.

    A nasa bangare, Modi ya bayyana cewa, ganawar da ya yi da shugaba Xi a Kazan ta nuna alkiblar ci gaban dangantakar Indiya da Sin, dangantakar ta koma kan hanyar kyau, iyakokin kasashen biyu sun kasance cikin kwanciyar hankali, kuma za a maido da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin kasashen 2 nan ba da jimawa ba. Wadannan nasarorin ba kawai sun amfanar al’ummar Indiya da Sin ba, har ma suna da amfani ga duniya baki daya. Indiya da Sin abokan hulda ne ba abokan hamayya ba, yarjejeniyoyi sun fi bambance-bambance, kuma Indiya tana son yin hangen nesa kan habaka dangantakar kasashen biyu.

    Bugu da kari, a wannan rana shugaba Xi ya gana da shugabannin wasu kasashe da suka zo nan kasar Sin don halarar taron, ciki har da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, shugaban Azerbaijan Ilham Heydar oglu Aliyev, firayim ministan Armenia Nikol Pashinyan, shugaban Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da shugaban Maldives Mohamed Muizzu,da Firaministan Vietnam Pham Minh Chinh kana da shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.(Amina Xu)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin

    [ad_1]



    Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025.

    Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC).

    Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba.

    Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a.

    Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja a mita 92.7 zangon FM, inda za ta kawo shirye-shiryen da za su ilmantar, wayar da kai, da kuma bayar da dama ga ‘yan Najeriya su bayyana ra’ayoyinsu kan batutuwa kamar mulki, ci gaba, al’adu da rayuwar yau da kullum.

    Trust Radio wani rukuni ne kamfanin Media Trust, wanda suke buga jaridar Daily Trust, waɗanda aka san su kan tsage gaskiya.

    Ana gayyatar jama’a a Babban Birnin Tarayya su saurari tashar, domin sauraren batutuwa da aka gina bisa gaskiya da adalci.


    [ad_2]

    Source link

  • Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO

    [ad_1]

    A daren yau 31 ga watan Agusta, Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan sun shirya liyafar maraba a cibiyar baje kolin kayayyaki ta Meijiang da ke Tianjin, don maraba da baki na kasa da kasa wadanda suka zo nan kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin kan Shanghai (SCO) na shekarar 2025.

    A cikin jawabin gaisuwar, Xi Jinping ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), ta kasance tana rike da “Ruhin Shanghai,” tana karfafa hadin kai da amincewa da juna, da kara zurfafa hadin gwiwa, kana da shiga cikin al’amuran kasa da kasa da na yanki, ta zama wata muhimmin karfi wajen inganta sabuwar dangantakar kasa da kasa da kuma gina kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya.

    A halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu a shekaru dari da suka gabata ba, halin rashin kwanciyar hankali, rashin tabbas, da kuma wahalhalu sun kara karuwa. Kungiyar SCO tana da babban alhakin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma habaka ci gaban da wadatar kasashe.

    Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori.

    Kafin liyafar maraba, Shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun yi maraba da shugabannin kasashen waje da matansu cikin fara’a, inda suka mika musu hannu tare da gaisawa, kuma suka dauki hotuna tare da su.(Amina Xu)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Gobarar Tankar Mai Ta Lakume Manyan Motoci 4 A Legas

    [ad_1]

    Wata tanka ɗauke da fetur (PMS) ta kife a ranar Lahadi a jihar Legas inda nan take ta kama da wuta. Gobarar ta bazu cikin sauri, ta laƙume aƙalla manyan motoci guda huɗu da aka ajiye a wajen Iyana-Isolo zuwa Oshodi.

    Daraktan sashin hulɗa da Jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA), Taofiq Adebayo, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna gudun wuce gona da iri ne ya sa direban ya rasa iko da motar, abin da ya haifar da mummunar haɗarin.

    Cikin gaggawa jami’an LASTMA, tare da haɗin gwiwar ma’aikatan kashe gobara da jam’ian ƴansanda daga Aswani, da Ilasa da Mushin, da ma jami’an tsaro na unguwanni ne suka yi aiki tukuru wajen shawo kan gobarar kafin ta girmama.

    Babban Daraktan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya tabbatar da cewa babu asarar rai, yana mai jaddada cewa hakan ya faru ne saboda saurin rufe hanyar da kuma dakatar da motoci daga Ilasa zuwa Oshodi. Ya gargadi direbobin manyan motoci da tankoki su kiyaye gudun wuce sa’a domin kare rayuka da dukiyoyi.

    Ya kuma buƙaci jama’a da su rika amfani da layin waya kyauta na LASTMA wajen sanar da kowanne irin hatsari ko matsalar hanya, domin hukumar ta ci gaba da kare lafiyar al’umma da kuma tabbatar da tsari a hanyoyin jihar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Farfado Da Kasa Bisa Karfin Ruhin Turjiya Ga Zalunci

    [ad_1]

    Za a wallafa makalar da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, game da ci gaba da aiki da karfin ruhin da aka samu a lokacin yakin turjiya ga zaluncin Japanawa a bisa hanyar neman farfado da kasa a mujallar Qiushi, wacce take babbar mujalla ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

    Yakin shi ne mafi tsawo kuma mafi girma da jama’ar kasar Sin suka yi da zaluncin kasashen waje a wannan zamanin, wanda ya zo da mafi girman sadaukarwa, amma ya kai ga nasarar farko da Sinawa suka samu wajen ‘yantar da kasa. Har ila yau, nasarar yakin ta kasance wani muhimmin sashe na nasarar da duniya ta samu a kan mulkin danniya.

    Kazalika, makalar ta yi nuni da cewa, sakamakon nasarar da aka samu ta yakin turjiyar jama’ar kasar Sin a kan zaluncin Japanawa da yaki da mulkin danniya a duniya ya zarce batun sabani kawai, kana ta ce, al’ummar kasar Sin da sauran al’ummomin duniya ba za su taba amincewa da duk wani yunkuri na musantawa, ko gurbata gaskiya, ko shafa fenti a kan tarihin mamayar ba.

    Ruhi mai karfi da aka samu a lokacin yakin turjiyar ya kasance wani muhimmin ginshiki mai karfi, wanda ya jagoranci jama’ar kasar Sin zuwa shawo kan wahalhalu da cikas a yunkurinsu na farfado da kasa, kamar yadda makalar ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link