Akalla mutane 15 ne aka ce sun rasu, yayin da wasu uku suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kife a kauyen Danmaga da ke karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara.
A wani bincike da LEADERSHIP ta gudanar, lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da wasu mazauna kauye kimanin 20 da suka tsere daga harin ‘yan bindiga suka shiga wani kwale-kwale da ya kife a lokacin da suke kokarin tsallakawa kogi a Nasarawar Kifi da ke unguwar Birnin Tudu.
Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su, galibinsu mata ne da kananan yara ‘yan kauyen Danmaga da Tungar Maigunya da kuma Nasarawar Kifi da suke neman tsira daga hare-haren ‘yan bindiga inda suka garzaya zuwa bakin kogi domin tsallakawa ta hanyar kwale-kwale.
A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shugaban Amurka, Donald Trump ya kakaba harajin kashi 50 cikin 100 kan kayayyakin Indiya da ake kai wa Amurka, wanda ladabatarwa ne kan kasar da ke cikin masu arziki a duniya saboda cigaba da sayen mai daga Rasha.
Wannan harajin zai iya yin gagarumin illa ga ‘yan kasuwa da tattalin arzikin Indiya.
Gwamnatin Delhi ta ce ba a yi musu adalci ba, sannan sayan mai da ta yi daga Rasha na da alaka da bukatun kasar.
Ana dai ganin wannan mataki na iya bai wa Indiya dama ta kusanci gwamnatin Moscow da kuma Beijing sosai.
Firaministan Indiya, Narendra Modi, zai je China a cikin makonnan, a wata ziyarar farko cikin shekaru bakwai, domin halartar taro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Wani tsoho mai suna Uchelue Ikechukwu mai shekaru 75 yana daga cikin mutane shida da ake zargi da hada-hadar miyagun kwayoyi a wani samame da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) suka kai a wasu sassan jihar Anambra.
Har ila yau, a wani samame daban, Hukumar ta kama Alfa Andrew dan shekaru 30 biyo bayan lalata masa gonar wiwi mai nauyin kilo 178,750 a garin Mayafi, karamar hukumar Sardauna, jihar Taraba.
Yayin da aka kama Uchelue a Umudioka, karamar hukumar Dunukofia ta jihar Anambra da miyagun kwayoyi kimanin kilo 26.7 a ranar Alhamis, 28 ga Agusta, 2025; Eneh Makuo; Emmanuel Chiemeli; Uwakwe Matthew; Chukwujekwu Ehirim; Ifeanyichukwu Olisa da Odoh Chukwuma, duk suna daga cikin mutanen da NDLEA ta cika hannun da su dauke da nau’ukan miyagun kwayoyi daban-daban duk a jihar ta Anambra.
Amma Andrew na jihar Taraba, an kama shi ne a ranar Talata, 26 ga watan Agusta lokacin da jami’an NDLEA da hadin gwiwar jami’an Sojin Nijeriya, da Hukumar Tsaron Daji, da kungiyar matasan Mambila da ‘yan banga, suka kai farmaki a gonarsa mai fadin hekta 71.5 ta tabar wiwi da ke dajin Mayodoga, gundumar Mayosabere a karamar hukumar Sardauna, jihar Taraba, inda suka lalata ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Tsohon Sufeto-Janar na rundunar ’yan sandan Nijeriya, Solomon Arase ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, babban birnin kasar.
Rahotanni sun ce tsohon IG din ya rasu ne a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja a safiyar Lahadin nan.
Kawo yanzu dai iyalai ko rundunar ’yan sandan kasar ba su fitar da rahoton rasuwar a hukumance ba, sai dai wani hadiminsa da Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da hakan.
Arase wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada a Afrilun 2015 shi ne Sufeto Janar na 18 a tarihin Nijeriya.
Kazalika, bayan ritayarsa a shekarar 2016, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar kula da harkokin ’yan sanda ta Nijeriya PSC a Janairun 2023, wanda kuma shugaba Bola Tinubu ya sauke a bara.
Tsohon Sufeto-Janar na rundunar ’yan sandan Nijeriya, Solomon Arase ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, babban birnin kasar.
Rahotanni sun ce tsohon IG din ya rasu ne a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja a safiyar Lahadin nan.
Kawo yanzu dai iyalai ko rundunar ’yan sandan kasar ba su fitar da rahoton rasuwar a hukumance ba, sai dai wani hadiminsa da Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da hakan.
Arase wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada a Afrilun 2015 shi ne Sufeto Janar na 18 a tarihin Nijeriya.
Kazalika, bayan ritayarsa a shekarar 2016, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar kula da harkokin ’yan sanda ta Nijeriya PSC a Janairun 2023, wanda kuma shugaba Bola Tinubu ya sauke a bara.
Mazauna sun lakaɗa wa wata mata duka sannan suka ƙone ta ƙurmus kan zargin yi wa fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) ɓatanci a yankin Kasuwan-Garba da ke ƙaramar hukumar Mariga ta Jihar Neja.
Shaidu sun ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da wata muhawara ta taso a cikin shagon matar inda take abincin sayarwa.
Aminiya ta ruwaito cewa, wani daga cikin kwastomomin matar ne cikin raha ya ce yana so ya aure ta domin ta zamo matarsa kamar yadda sunnar Ma’aiki (SAW) da tanadar, amma daga bisani lamarin ya haifar da cece-kuce har aka yi zargin ta furta kalaman ɓatanci.
Wani da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce an fara kai matar fadar Hakimin Kasuwan-Garba, inda daga nan aka miƙa ta hannun jami’an tsaro domin bincike.
Sai dai wasu gungun fusatattun matasa suka kwace matar mai suna Amaye daga hannun jami’an tsaron suka riƙa jifa da dukan da ya yi ajalinta.
Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa yanzu haka ƙura ta lafa kuma harkokin yau da kullum sun kankama.
Kazalika, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa “da misalin ƙarfe 2 na ranar 30 ga watan Agusta, an samu rahoto cewa wata mata mai suna Amaye ta yi wasu kalamai da aka ɗauka a matsayin ɓatanci ga Annabi (SAW).
“Wannan lamari ya jawo fushin jama’a da suka kai mata farmaki suka ƙone ta kafin isowar ƙarin jami’an tsaro.
“Yanzu haka ana ƙoƙarin cafke waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin gudanar da bincike da gurfanar da su a kotu.”
A watan Yuli, wani jami’in hukumar makamashi na Rasha ya ziyarci Jamhuriyar Nijar don sanya hannu kan yarjejeniyar inganta makashi tsakanin kasashen biyu.
Yarjejeniyar ta tsara hanyoyin da kasashen biyu za su iya hadaka a bangaren wutar lantarki da magunguna da horar da ma’aikata.
Wannan ya nuna cewa Rasha na kara kutsawa cikin kasar, wadda ke cikin wadanda suka fi yawan ma’adanin yureniyom (uranium) a duniya, da ma sauran kasashen yankin Sahel a nahiyar ta Afirka.
Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu.
Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin taimakon kasashen da makamai da horo.
Amma ganin yadda har yanzu kasashen ke ci gaba da fuskantar hare-hare, shin za a iya cewa alaka da Rasha ta yi musu rana?
Sababbin kawayen Moscow
Tun a 2021 Rasha ke tura dubban sojoji da makaman da suka kai miliyoyin Dala zuwa Mali da Burkina Faso da Nijar.
Tana haka ne domin taimakon kasashen wajen yaki da matsalolin tsaro da ya dabaibaye yankin Sahel, inda kungiyoyin ‘yanbindiga masu ikirarin jihadi ke amfani da raunin gwamnati da talauci da kiyayyar gwamnatotin kasashen yamma da rikice-rikicen kabilanci a kasashen wajen kutsawa.
Sojojin hayar na Rasha sai suka samu shiga, inda gwamntocin soji a kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka rika daga tutar Rasha a tarukansu, wanda hakan ke nuna goyon bayansu da agajin Rasha.
Hakan ya sa kasashen uku suka nisanta kansu daga Faransa, wadda ita ce ta raine su a baya, da ma wasu kasashen na yamma.
Ba kamar sauran kasashen na yamma ba, ita Rasha ta tura musu dakaru da makamai ba tare da wasu sharuda ba, wanda a lokuta da dama ke zuwa da alkawarin tabbatar da mulkin dimokuradiyya.
Dakarun Wagner na Rasha sun isa Mali ne a 2021 bayan sojojin Faransa sun fice daga kasar, inda a shekarar 2023 sojojin Mali tare da taimakon dakarun Wagner suka kwace wani babban sansanin ‘yanwataye da ke arewacin kasar.
Amma tun bayan wannan nasarar, hare-haren kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal Muslimin (JNIM) mai alaka da al-Kaeda sai suka karu.
A 2024, sama da mutum 70 ne suka rasu, sannan sama da 200 suka ji rauni a harin JNIM a babban birnin Mali, Bamako.
“Zuwan dakarun Wagner bai dakile harkokin kungiyar JNIM ba,” a cewar Hani Nsaibia ta kungiyar ACLED.
A 2023 ne Yebgeny Prigozhin, jagoran Wagner ya rasu a hadarin jirgin sama kwanaki kadan bayan ya yi yunkurin kifar da gwamnatin Bladimir Putin a Rasha.
Sai gwamnatin Rasha ta yi wa dakarun garambawul, sai suka koma dakarun Afirka wato Africa Corps.
A watan Yunin bana ne dakarun na Wagner suka sanar da ficewarsu daga Mali, inda suka ce sun kammala aikin da ya kawo su.
A wani sako da suka fitar a Telegram, sun ce sun “kashe dubban ‘yantawaye da shugabanninsu da suka dade suna addabar fararen hula.”
Ci gaba da rikice-rikice
Kamar yadda alkaluman Global Terrorism Inded suka nuna, sun ce yankin Sahel ne “cibiyar ta’addanci” na duniya, kuma a yankin ne aka samu kusan rabin mutuwa da k da alaka da ta’addanci a duniya, wanda ya sa ake tambayar amfanin shigar Rasha cikin lamarin.
Haka kuma gabashin Mali da Burkina Faso sun dade suna fama da matsalar tsaro tun wajajen 2025.
ACLED ta ce an kashe sama da mutum 20,000, sannan sama da miliyan sun rabu da muhallansu.
A Nijar, akwai gomman sojojin Rasha da suke aiki tare da sojojin kasar, amma har yanzu babu wata nasarar a-zo-a-gani.
A watan Maris na bana, an kashe sama da mutum 40 a wani hari da aka kai a masallaci a yammacin Nijar.
Masanin tsaro Adib Saani ya ce mayakan Nijar da Mali da Burkina Faso sun kara kaimi ne saboda ficewar kasashen yamma.
Andre Lebobich, wani mai bincike a cibiyar Clingendael Institute da ke Netherlands, ya ce sojojin Rasha da ke yankin Sahel aiki ya musu yawa, wanda hakan ne ma a cewarsa ya sa JNIM suka fadada zuwa ksashen Togo da Benin.
Rashin karfin soji
Kwararre a fannin tsaro a Yammacin Afirka Hani Nsaibia ya ce sojojin Rasha da ke aiki a yankin Sahel sun yi karanci, wanda hakan ya sa yake ganin ba sa samun nasara.
Rahotanni sun ce an janye wasu sojojin Rasha saboda yakin Ukraine, wanda hakan ya haifar da gibi saboda babu sojojin wanzar da zaman lafiya daga kasashen yamma ba.
“Zai yi wahala sojojin Rasha 2,000 su iya maye gurbin sojojin wanzar da zaman lafiya kimanin 18,000 da ke aiki a yankin a baya,” in ji shi.
A wani taron tsaro a watan jiya, ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Labrob ya nanata cewa kasar za ta ci gaba da taimakon kasashen Afirka domin wanzar da zaman lafiya.
Amma masana na ganin magana kawai ba za ta iya wadatar ba, “domin mutanen yankin da dama suna rayuwa ne a kullum a kasa da dala, ga kuma rashin ababen more rayuwa,” in ji masanin tsaron Ghana, Adib Saani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan gaban Manchester United, Alejandro Garnacho, kan kuɗin da ya kai kusan fam miliyan 85 (£85m).
Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan na ƙasar Argentina ya rattaba hannu kan kwantiragin zama a Stamford Bridge har zuwa shekarar 2032.
Garnacho, mai shekara 21, zai riƙa ɗaukar albashin fam 250,000 duk mako, kwatankwacin Naira miliyan 500 a kuɗin Nijeriya, lamarin ya sanya shi a sahun manyan ’yan wasa mafiya albashi a Stamford Bridge.
A bara ne tauraruwarsa ta haska a Manchester United, bayan ya ci ƙwallo 11 ya kuma ba da gudunmawar zura wasu 10 a raga.
A jimilla, ya buga wasanni 144 tun daga lokacin da aka ɗaukoshi daga Atlético Madrid a 2020, inda ya ci ƙwallo 26.
Ana iya tuna cewa Garnacho yana cikin ’yan wasa biyar da suka nemi barin United, ciki har da Marcus Rashford, Antony, Tyrell Malacia da Jadon Sancho, bayan wata matsala da ta shafi sabon tsarin koci a Old Trafford.
Kociyan Chelsea, Enzo Maresca, ya bayyana farin ciki da wannan cafane da aka yi, inda ya ce Garnacho zai ƙara wa ƙungiyar kuzari da saurin kai hare-haren a wasanninta.
“Ɗan wasa ne da yake iya sauya salon wasanni da kansa, kuma hakan zai taimaka wajen dawo da Chelsea cikin sahun manyan ƙungiyoyin masu neman kofuna,” in ji shi.
Masu sharhi sun ce wannan matakin zai ƙara armashi da zafi a gasar Premier League, musamman ganin yadda Garnacho ya saba taka rawar nuna kansa a manyan wasanni.
Sai dai da dama daga cikin magoya bayan Manchester United sun nuna takaicinsu kan cefanar da ɗan wasan da aka yi, inda suke ganin bai kamata a sayar da shi ba saboda a gina ƙungiyar da shi tare da sauran matasan ’yan wasan da ke nuna hazaƙa.
Kawo yanzu dai kungiyoyin gasar Premier League ta Ingila sun kashe sama da fan biliyan biyu a bazarar nan, amma har yanzu akwai cinikin da ba a kammala ba kafin rufe kasuwar a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, wanda kuma daga nan ne idan aka rufe kasuwar ba za a sake budewa ba sai a cikin watan Janairu na sabuwar shekarar 2026 kamar yadda a dokar hukumar kwallon kafa ta duniya.
Tuni sababbin ‘yan wasan da suka samu shiga wasu daga cikin kungiyoyi sun fara bayyana kawunansu ta hanyar zura kwallaye a raga kamar yadda muka ga yadda dan wasa Hugo Ekitike ya zura kwallaye biyu cikin wasanni biyu da ya buga a gasar Firimiya da kuma dan wasa Biktor Gyokeres wanda shima ya zura kwallaye biyu a was ana biyu da ya bugawa Arsenal.
Sito na makamai
Yayin da ake tunanin Arsenal ta kammala komai bayan daukar ‘yanwasa ciki har da lamba 9 Biktor Gyokeres. Sai kuma lissafi ya sauya saboda raunin da danwasan gaba Kai Habertz ya ji, wanda ya sa ta fara neman danwasan Crystal Palace Eberechi Eze, wanda tuni ya rattaba hannu a kan kwantiragin shekara biyar kuma zai saka riga mai lamba goma a sabuwar kungiyar tasa.
Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta dauki danwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu. Bayan da cinikin Eze ya fada, yanzu kuma kungiyar ta Arsenal ta sake mayar da hankalinta wajen sayan dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafa ta Bayer Liberkusen, wato Piero Hincapie.
Chelsea
Da alama har yanzu mai horarwa Enzo Maresca bai hakura da karin cefane ba kafin rufe kasuwar, yayin da yake neman Alejandro Garnacho na Man United da danwasan RB Leipzig Dabi Simons. Sai dai komai zai dogara ne da yawan ‘yanwasan da ta iya sayarwa kamar Nicolas Jackson da Christopher Nkunku da Tyrikue George, wadanda duka kungiyar ta saka a kasuwa. Kociyan zai kuma so ya karfafa bayansa saboda yadda aka ce Lebi Colwill ba zai buga mafi yawan gasar bana ba saboda rauni a gwiwarsa.
Crystal Palace
Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ba ta yi wata sayayyar kirki ba zuwa yanzu, amma ana sa ran abubuwa za su sauya nan gaba kadan saboda mai horarwa Oliber Glasner na neman danwasan gaba da na baya. Za a yi yunkurin ne saboda makomar ɗanbaya kuma kyaftin dinta Marc Guehi, wanda Liberpool da Manchester City suke zawarci sai kuma danwasan gaba Eberechi Eze, wanda tuni ya koma Arsenal. Ana ci gaba da alakanta Palace da Jeremy Jackuet na Rennes, yayin da kuma take harin danwasan tsakiya Bilal El Khannouss na Leicester City.
Liverpool
Mai koyar da ‘yan wasan Liberpool Arne Slot ya samu kudaden cefane masu yawa a bana wadanda ya sayi Florian Wirtz, da Jeremie Frimpong, da Milos Kerkez, da Hugo Ekitike, da Giobanni Leoni. Amma duk da haka yana fatan sake kashe miliyoyi wajen maye gurbin danwasan baya Jarell Kuansah da kuma sama wa Birgil ban Dijk abokin aiki. Ana sa ran za ta nemi Marc Guehi na Crystal Palace. Sai kuma turka-turkar sayen danwasan gaba Aledander Isak daga Newcastle, wanda har yanzu Liberpool bata fitar da ran za ta saya ba.
Manchester City
Manchester City ta sayi mafi yawan ‘yanwasanta tun kafin gasar Club World Cup, kuma wasu majiyoyi sun bayyana cewa ta gama sayayya. An yi ta rade-radin cewa tana son daukar mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain Gianluigi Donnarumma, amma tabbas wannan zai danganta ne da mai tsaron raga Ederson, wanda ake ganin shima zai iya barin kungiyar. Tottenham ta nuna sha’awar daukar Sabinho amma City ta ki amincewa zuwa yanzu. Amma idan ta yarda to hakan zai iya ba ta damar sayen danwasan Real Madrid Rodrygo.
Manchester United
Shima mai koyar da ‘yanwasan Manchester United Ruben Amorim ya mayar da hankalinsa kan bangaren gaba na tawagar tasa inda ya kashe fan miliyan 200 zuwa yanzu domin sayen Matheus Cunha, da Bryan Mbeumo, da Benjamin Sesko. Amma a bayyane take cewa United na da matsala a mai tsaron raga, yayin da Andre Onana ya gaza kuma shi ma Altay Bayindir ya fara aikata manyan kurakurai a wasansu da Arsenal. United na tunanin daukar Senne Lammens na Royal Antwarp.
Newcastle United
Har yanzu makomar Aledander Isak na cikin kokwanto duk da yunkurin mai horarwa Edie Howe na karfafa tawagarsa. Zuwa yanzu kungiyar ta sayi Anthony Elanga daga Bournemouth, da Jacob Ramsey daga Aston Billa, da Malick Thiaw daga AC Milan, kuma har yanzu kungiyar tana neman sayan dan wasan gaba kafin ta saki Aledandre Isak.
Yanzu dai kungiyar ta kwallafa kan Yoane Wissa amma kuma tana fuskantar turjiya daga Brentford saboda yadda ta ki yarda da tayin fan miliyan 40 kan dan wasan mai shekara 28 a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Tuni aka fara kakar wasa ta shekara ta 2025 zuwa 2026 ta gasar Premier League ta Ingila inda aka ci gaba a ranar Juma’a 14 ga watan Agustan wannan shekarar kuma mai kare kambu, kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ce ta fara wasa a gida a wasan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth da ci 3-2 a filin was ana Anfield dake birnin Liberpool.
Tauraron danwasan kasar Masar Mohamed Salah, shi ne gwarzon danwasan gasar kuma zai yi yunkurin lashe takalmin zinare na biyar yayin da zai fara buga wasa da sababbin ‘yanwasan da kungiyar ta saya da suka hada da Hugo Ekitike da Florian Wirtz da Jeremi Frimpong da Leon da Milos Kerkez.
Wasu ‘yanwasan Afirka da dama sun samu komawa manyan kungiyoyi, akwai kuma wasu sababbi a gasar daga kasashen Kongo, da Morocco, da Mozambikue, da Senegal. A gefe guda kuma, ‘yanwasan nahiyar kusan 50 ne za su bar wasannin gasar zuwa gida domin karawa a gasar Kofin kasashen Afirka ta 2025 (Afcon 2025) da za a yi daga 21 ga watan Disamba zuwa 18 ga Janairu.
Ko Mbeumo zai dawo wa United da karsashinta?
Dan wasan dan kasar Kamaru Bryna Mbeumo ya zama abin tattaunawa kuma mafi tsada a ‘yanwasan Afirka lokacin da ya koma Manchester United kan fani miliyan 65 daga kungiyar kwallon kafa ta Brentford. Dan kwallon mai shekara 25 ya ci kwallo 20 a gasar da aka kammala da kuma bayarwa a ci bakwai. Manchester United na tsaka da sake gina kungiyar karkashin mai horarwa Ruben Amorim bayan gama gasar a mataki na 15, wanda shi ne mafi muni a tarihin kungiyar na Premier League.
Mbeumo zai fuskanci matsi nan take domin ya nuna kwarewarsa tare da Matheus Cunha da Benjamin Sesko wadanda duka kungiyar ta sayo a wannan kakar domin kara karfin ‘yanwasan gabanra da kuma kokarin ci gaba da zura kwallaye a raga duk da cewa bayan buga wasanni biyu a gasar firimiya har yanzu babu daya daga cikinsu da ya zura kwallo a raga.
Wani babban cinikin da aka yi shi ne wanda dan wasa Mohammed Kudus ya kawo karshen zaman shekara biyu da ya yi a kungiyar West Ham kuma ya koma Tottenham kan fan miliyan 55. Danwasan na Ghana ya taka rawa sosai a West Ham a kakar farko, amma bai yi kokari ba a kaka ta biyu saboda yadda ya yi fama da salon wasa na mai horarwa Graham Potter.
Irin kokarin da dan wasan mai shekara 24 din ya yi shi ne ya sa kungiyoyi da dama suka dinga nemansa, kuma yanzu Tottenham za ta so ya nemo wannan bajintar tasa domin taimaka mata a sabuwar kaka. Saboda samun damar buga gasar zakarun Turai ta Champions League na daya daga cikin dalilan da suka sa ya koma kungiyar Tottenham ta birnin London.
Yayin da tauraron danwasa Son Heung-Min ya bar kungiyar, da kuma James Maddison da ya ji rauni, Kudus zai iya zama mai muhimmancin gaske tun daga farkon kaka.
Ko Ait-Nouri zai taimaki Man City dawo da martabarta?
Bayan komawa mataki na uku da kuma kammala kakar 2024 zuwa 2025 ba tare da wani kofin kirki ba, Manchester City za ta danno da karfinta domin daukar kofi. Kungiyar ta shiga kasuwa da wurwuri domin daukar danwasan baya daga bangaren hagu Rayan Ait-Nouri, kuma danwasan mai shekara 24 ya fara buga mata wasa a gasar Club World Cup da ba ta je ko’ina ba. Dab wasan dan kasar Aljeriya ya koma Manchester City ne daga Wolbes a kan kudi fam miliyan 31.
Ait-Nouri ya nuna barazanar kai hari sosai daga gefensa duk da yadda Wolbes ta sha fama a kakar bara, inda ya ci kwallo hudu da kuma bayar da bakwai a zira a raga. Bayan ya samu wuri a Manchester City, tabbas mai horarwa Pep Guardiola zai so sabon mutumin nasa ya kara wuta wajen jawo kwallo daga baya zuwa gaba, sai dai bai taimakawa kungiyar ba a wasan da suka yi Rashin nasara a hannun Tottenham a ranar Asabar.
Adingra a Sunderland. Kungiyar Sunderland ta dawo buga gasar Premier League a karon farko tun 2017, kuma tuni ta karade kasuwar sayen ‘yanwasa, har ma ta sayi 11.
Shida daga cikinsu ‘yan Afirka ne. Ta kashe kudi mafi yawa a tarihinta fan miliyan 30 kan dan kasar Senegal Habib Diarra, da daukar Arthur Masuaku da Noah Sadiki ‘yan kasar Kongo, da dan Mozambikue mai suna Reinildo, da Chemsdine Talbi na Morocco.
Simon Adingra da ya ci kofin Afcon 2023 da kasarsa Ibory Coast na cikin mutanen da ya sauya sheka daga kudu zuwa arewaci bayan fara wasa 12 kacal a kakar bara. Yayin da yake cikin ‘yanwsan da suka san Premier League, dan kwallon mai shekara 23 zai so ya taimaka wa Sunderland ci gaba da zama a gasar.
Har yanzu West Ham za ta ci gaba da aiki da dan Afirka bayan ta biya fan miliyan 19 wajen daukar El Hadji Malick Diouf daga Slabia Prague.
Kociyan kungiyar Graham Potter ya ce dan wasan Senegal din mai shekara 20 yana da yunwar buga wasa da kuma buri mai yawa saboda haka za su taimaka masa wajen cika burinsa kuma West Ham United ce kungiyar da zai samu wannan damar.
Shima danwasan Kongo Aedel Tuanzebe zai so ya sake guje wa barin gasar ta Premier a karo na biyu bayan ya koma Burnley daga Ipswich Town. Ganin cewa sai a ranar 1 ga watan Satumba za a rufe kasuwar saye da musayar ‘yan kwallon, akwai ‘yanwasan Afirka da za su motsa a bana zuwa Premier.
Dan wasan Senegal da Chelsea, Nicolas Jackson ya samu izinin barin Chelsea a kasuwar nan, yayin da shi ma na Kongo Yoane Wissa ke shirin barin Brentford zuwa Newcastle United.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe