Category: Latest News

  • NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Da Mutane Zasu Bi Wajen Neman Diyya

    [ad_1]

    Karin fannoni



    Sau da dama ibti’lai kan faru da wasu mutane wanda ya kamata ace sun bi hanyoyi don a biya su diyya.

    Sai dai masana na bayyana cewa sau da dama mutane basu san honyoyin da ya kamata subi don neman hakkokin su ba.

    Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da mutane zasu bi don neman diyya idan an zalunce su.

    Domin sauke shirin, latsa nan


    [ad_2]

    Source link

  • An kama masu safarar muggan makamai a Katsina

    [ad_1]



    ’Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da safarar makamai masu haɗarin gaske, tare da tarin harsasai, a wani samame a Jihar Katsina.

    A farkon wannan mako ne ’yan sanda da ke sintiri suka tare wata mota ƙirar Volkswagen Golf, da asubahi, inda suka  gano bindiga ƙirar GPMG da sauran makamai a cikinta a kan hanyar Ingawa zuwa Karkarku.

    Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Dakta Nasir Mu’azu, ya sanar da cewa masu safarar makaman matasa ne masu shekara 12 da kuma 25, daga ƙauyen Ɓaure a Ƙaramar Hukumar Safana ta jihar.

    Makaman da aka gano

    Sun shiga hannun hukuma bayan da aka gano suna ɗauke da wata babbar bindigar sojoji mai haɗarin gaske, ƙirar GPMG.

    Jami’an sun kuma gano harsasai guda 1,063 na bindigar AK-47 da kuma harsasai 232 na PKT a hannun matasan.

    Binciken farko ya nuna cewa makaman sun fito ne daga Haɗejia, Jihar Jigawa, kuma ana nufin kai su zuwa Safana, Katsina.

    Kwamishinan ya ce, “Ana bincike yana domin gano ƙarshen inda makaman za su kai, da kuma sauran abokan safarar makaman da kuma inda aka samo su.”

    Matsakar tsaro a Katsina

    Katsina ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da ke satar mutane domin neman kudin fansa da kuma safarar makamai.

    Wannan ya sa hukumomi ke ƙara shirin karfafa tsaro da kuma yin sintiri a hanyoyin shiga da fita daga jihar.

    Gwamnatin jihar ta yi kira ga jama’a su ci gaba da bayar da rahoto idan sun ga wani abu da ba su fahimta ba, musamman game da motsin ’yan bindiga da masu safarar makamai a yankunan karkara.


    [ad_2]

    Source link

  • ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Daba 107 A Kano, Sun Ƙwato Makamai Da Ƙwayoyi

    [ad_1]

    Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta kama mutane 107 da ake zargi da aikata laifuka tare da ƙwato makamai masu hatsari 473 da kuma tarin miyagun ƙwayoyi.

    Kwamishinan ’Yansandan Jihar, Ibrahim Adamu Bakori ne, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake bayani ga manema labarai kan nasarorin Operation Kukan Kura, wanda aka fara a watan Yuli 2025.

    A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifuka irin su fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, fɗan daba, da sauran laifuka.

    Ya ce aikin ya taimaka sosai wajen rage yawan laifukan daba, wanda shi ne babban matsalar tsaro a jihar.

    Kwamishinan ya ƙara da cewa Operation Kukan Kura na haɗa al’umma da ’yansanda ta hanyar bayar da bayanai da goyon baya.

    Ya ce wannan dabara, wadda ta yi kama da tsarin ‘community policing’, ta tabbatar da inganci wajen rage laifuka a jihar.

    A cikin watan Agusta kaɗai, ’yansanda sun ƙwato fakiti 485 na ganyen tabar wiwi, kwalaye 211 na wasu kayan maye, kwalabe 257 na maganin kashe ɓeraye, da kuma ƙwayoyi 21 na Exol.

    Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da wayoyi 59, POS guda uku, katin cirar kuɗi na banki 17, na’urar MP3 guda uku, tare da bindigogi, harsasai da sauran makamai masu hatsari.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • An kai wa tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami hari a Kebbi

    [ad_1]



    Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari.

    Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa, Kodayake babu asarar rai.

    Bayan dawowar tsohon ministan a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari,  gida ya yi zargin siyasa ce ta a da aka kai masa harin, yana mai jaddada cewa, harkar siyasarsa babu gudu babu ja da baya.

    “Shari’a ta tanadi ka kare kai, in aka kawo maka hari amma kai kar ka kai wa kowa hari, maganar siyasa ba gudu ba ja da baya.

    “Muna da hakkin kare kai in an ture mu, kariyar kai a shari’ar Musulunci hakki ne, mai girma Gwamna ya ce ya bude littafin siyasa mu ko mun fara karatu,” a cewar Malami, a jawabinsa ga magoya bayansa.

    Ya zargi magoya bayan Jam’iyyar APC da kai masu hari, “addini ya aminta mu yi wa ’yan uwa jaje in sun samu rashi, shi ne maƙasudin yin wannan ziyara a garin Birnin Kebbi, bakin abubuwa marasa dadi sun bayyana wadanda suke da nasaba da siyasa, bayyane take mutane sun fito daga hedikwatar Jam’iyyar APC ɗauke da miyagun makamai suna jifan abokan hamayya.”

    Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar  Kebbi Yakubu Ahmed ya ce ba zai ce komai ba kan zargin, magana ce ta jam’iyya don haka a tuntube jami’yya.

    Wakilinmu ya tuntubi Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kana a waya amma bai daga ba, ya kuma tura masa sako bai ce komai ba, ya sake kiran sa, amma ya ji ‘number busy.’

    Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kebbi, Bello Sani,  ya ce ba wani da aka kama kan harin da aka kai wa tawagar tsohon minista Malami.

    A lokacin da yake magana da manema labarai bayan ya kammala zama da Gwamna kan matslar tsaro, Kwamishinan ’yan sandan ya ce ana gudanar da bincike kan abin da ya faru.

    A cewarsa, gwamnan ya kira taro kan tsaro game da abin da ya faru a unguwar G.R.A inda wasu ’yan jami’yyu suka karya doka da yin wasu al’amurran yakin neman zaɓe.

    Ya ce “dole ne mu gayyaci jam’iyun siyasa mu tattauna don su san har yanzu ba a dage shingen fara yekuwar zabe ba.”

    Kwamishina ya ce ’yan sanda sun sanya dakaru da za su hana duk wani yekuwar zaɓe don haka yana kira ga jam’iyyun siyasa su kwantar da hankalinsu.

    “Abin da ya faru ana kan bincike kuma duk wanda aka samu da laifi za a kama shi ya fuskanci Shari’a,” in ji Kwamishina.


    [ad_2]

    Source link

  • Xi Ya Gabatar Da Shawarar Tsarin Shugabanci Na Duniya

    [ad_1]

    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) Plus a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin a yau Litinin.

    Xi ya gabatar da shawarar Tsarin Shugabanci na Duniya mai lakabin “GGI” a taron, inda ya bayyana wasu ka’idoji guda biyar domin tsarin na GGI wanda ya ce, na farko ya kamata mu bi tsarin daidaito a kan ‘yancin yankunan kasa sau da kafa, na biyu ya kamata mu kiyaye bin dokokin kasa da kasa, na uku ya kamata mu aiwatar da tsarin mu’amala da bangarori daban daban, na hudu kuwa ya kamata mu yi yekuwar amfani da tsarin da zai fi mayar da hankali a kan al’umma, kana na biyar ya kamata mu mai da hankali kan daukar matakai na hakika.

    Xi kuma ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar SCO da su ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da ci gaba da kiyaye ka’idojin zama ‘yan ba ruwanmu, da kauce wa tayar da husuma kuma ba tare da kulla makirci ga wani ba, da mikewa tsaye wajen sauke nauyin hadin gwiwa mai bude kofa ga kasashen duniya, da daukar matakai na kare daidaito da adalci a fagen kasa da kasa.

    Kazalika, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin hada karfi da karfe wajen kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu, da samar da karin alfanu ga daukacin bil’adama ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Girgizar ƙasa ta hallaka fiye da mutum 800 a Afghanistan

    [ad_1]



    Mutum sama da 800 sun mutu, yayin da wasu fiye da 2,500 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6 da ta auku a lardin Kunar da ke gabashin Afghanistan, kusa da iyakar Pakistan.

    Girgizar ƙasar wadda ta auku da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadi ta rusa gidaje da dama da aka gina da laka da duwatsu, lamarin da ya sanya dubban mazauna kwana a waje.

    Rahotanni sun ce yara da mata na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu, kuma tuni an yi jana’izarsu.

    Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya bayyana fargabar cewa adadin waɗanda suka mutu ko jikkata na iya ƙaruwa domin akwai da dama da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa wasu ƙauyukan da abin ya fi shafa ba za a iya kai musu agaji ba saboda hanyoyin da suka toshe.

    Shugaban MDD, Antonio Guterres, ya miƙa ta’aziyarsa ga al’ummar Afghanistan cikin wata sanarwa da ya ce “ina goyon bayan da ƙara wa al’ummar Afghanistan ƙwarin gwiwa a wannan lokaci mai tsanani.”

    Shi ma shugaban cocin Katolika na Vatican, Fafaroma Leo XIV, ya bayyana a wata sanarwa cewa ya “yana matuƙar baƙin ciki da rayukan da suka salwanta a sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a gabashin Afghanistan.”

    A daren nan ne, ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Afghanistan da UAE suka yi shiru na minti ɗaya domin girmama waɗanda suka rasa rayukansu, kafin fara wasan ƙetaren ƙasa a Sharjah.

    Girgizar ƙasar ba ita farau ba

    Afghanistan dai na cikin ƙasashen da ke yawan fuskantar girgizar ƙasa, musamman a yankin tsaunukan Hindu Kush.

    Tun daga shekarar 1900, an samu girgizar ƙasa guda 12 da ƙarfinta ya haura maki 7 a yankin arewa maso gabas na ƙasar, a cewar Brian Baptie, wani masani a Birtaniya.

    “Wannan irin girgiza, haɗe da haɗarin bala’o’i da kuma irin ginin da ke yankin, na iya haddasa asarar rayuka masu yawa,” in ji shi.

    A watan Oktoba na 2023, girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.3 ta girgiza lardin Herat da ke yammacin ƙasar, inda mutane sama da 1,500 suka mutu, kuma gidaje sama da 63,000 suka lalace ko rushe.

    A watan Yuni na 2022, girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.9 da ta auku a lardin Paktika, an rasa rayuka fiye da 1,000 kuma dubban mutane suka rasa matsuguni.

    Bayan shafe shekaru 40 tana yaƙi, Afghanistan na fuskantar manyan ƙalubalen jin ƙai.

    Tun bayan dawowar Taliban a shekarar 2021, tallafin ƙasashen waje ya ragu sosai, lamarin da ya sa ƙasar ke samun cikas wajen ɗaukar matakan gaggawa idan bala’i ya auku.

    A halin yanzu dai Afghanistan na daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya, tana fama da mummunan rikicin jin ƙai, yayin da dubban ‘yan Afghanistan da aka mayar daga Pakistan da Iran suka koma gida cikin wannan shekara.

    Kimanin kashi 85 cikin ɗari na al’ummar Afghanistan na rayuwa da ƙasa da dala ɗaya a rana, a cewar Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP).


    [ad_2]

    Source link

  • Tottenham Ta Dauki Aron Kolo Muani Daga PSG

    [ad_1]

    Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta amince da daukar dan wasan Paris St-Germain Randal Kolo Muani a matsayin aro na tsawon kakar wasa daya, an dade ana danganta dan wasan mai shekaru 26 da kungiyoyin Firimiya, inda ake tsammanin yaje daya daga cikin kungiyoyin Tottenham, Manchester United, Chelsea ko kuma West Ham.

    Kolo na shirin komawa Tottenham a ranar karshe ta kasuwar saye da sayarwar yan kwallo bayan kulla yarjejeniyar a sirrance da kungiyar da Thomas Frank ke jagoranta, Kolo Muani ya shafe rabin kakar wasan da ta gabata a matsayin aro a Juventus, inda ya zura kwallaye takwas a wasanni 16 na Seria A.

    Tsohon dan wasan gaban Nantes da Eintracht Frankfurt ya koma PSG ne a watan Satumban 2023 kuma ya lashe gasar Ligue 1 har sau biyu, Kolo ya kuma buga wa Faransa manyan wasanni 31, inda ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya da ta doke Morocco a wasan dab da na kusa da karshe na shekarar 2022, ya kuma buga wasan karshe da Argentina ta doke su.

    Yana shirin zama babban dan wasa na hudu da Tottenham ta dauko a bazara, bayan Mohammed Kudus, Joao Palhinha da Xavi Simons, dan wasan gaban Kolo Muani zai taimakawa Tottenham wajen zura kwallaye yayinda take fatan komawa kan ganiyarta da kuma samun gurbin buga gasar Zakarun Turai a badi.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Ƙarin Kasafin Naira Biliyan 215.3 A Na 2025

    [ad_1]

    Majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin ta amince da karin kasafin kudi na naira biliyan 215.3 na kasafin kudi na shekarar 2025, wanda ya kai jimlar kasafin jihar zuwa sama da naira biliyan 935.

    Amincewar ta biyo bayan amincewa da bukatar Gwamna Abba Yusuf, wadda aka karanta a zaman taron makon jiya wanda kakakin majalisar Jibril Falgore ya jagoranta.

    Da yake sanar da kudurin, Falgore ya ce ‘yan majalisar sun yi muhawara sosai kan karin kasafin kudin kafin su amince.

    Ya ba da tabbacin cewa, Majalisar za ta kara sanya ido domin tabbatar da gaskiya da rikon amana ga yadda ake sarrafa kudaden jihar.




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan

    [ad_1]

    A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya.

    Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)




    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

    Shiga zaurenmu na WhatsApp



    [ad_2]

    Source link

  • An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe a Gombe

    [ad_1]



    Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe.

    Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin.

    Mai magana da yawun hukumar a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya ce bisa binciken da suka gudanar, uban da ɗan sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban.

    A cewarsa, Ibrahim Haruna wanda tela ne ya yi aika-aika ne a shagonsa na ɗinki, yayin da ɗansa kuma ya aikata laifin a cikin gidan da suke zaune.

    “Mun kammala binciken da muke gudanarwa, kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci,” in ji Sa’ad.

    Sai dai Ibrahim Haruna, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa kawai ya taɓa yarinyar ya yi a cikin wasa, amma bai yi mata fyaɗe ba.

    Hukumar ta ɓoye sunan yarinyar da abin ya shafa don kare mutuncinta da kuma ƙa’idojin kare haƙƙin yara da dokokin kare ‘yancin ɗan Adam suka tanadar.


    [ad_2]

    Source link