Batutuwan Da Suka Ci Wa ‘Yan Adawa Tuwo A Ƙwarya A Siyasar 2025

[ad_1]

Yusuf Shuaibu

Ga jam’iyyun adawa a Nijeriya, ana iya tuna shekara ta 2025 a matsayin shekara da ta fi ci wa ‘yan adawa tuwo a kwarya, wadda ta yi fice da sauyin sheka masu daukar hankali da rikice-rikicen cikin gida masu hana aiki a cikin jam’iyyu adawa, a yayin da jam’iyyar da ke mulki ta APC ke kara karfafa iko kafin 2027.

Daga jam’iyyar PDP zuwa LP da NNPP har ma da kananan jam’iyyu kamar irisu SDP, dukkan jam’iyyun adawan na fama da rarrabuwar kawuna fiye da yadda aka saba gani.

Jam’iyyu adawan sun fuskaci rarrabuwan kai da shari’o’i a kotu da sauya sheka mafi yawa zuwa APC, sun raunana tsarin jam’iyyun adawa, sannan sun rage aminci a wurin jama’a, wanda ya bar ‘yan adawa cikin dimuwa kusan shekaru biyu kafin babban zaben 2027.

A wannan yanayi ne ta kai ga bayyanar hadakar jam’iyyar ADC a watan Yuli, wanda ya samar da wani yanayi na sa ran samun gyara tafiyar jam’iyyun adawa a wani lokaci, duk da cewa akwai shakku game da dorewarta.

Matakin Kawancen Jam’iyyun Siyasa Da Raunin Adawa

Tun bayan rashin nasara a zaben shugaban kasa na 2023 a hannnun Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na ci gaba da jayayya cewa sai an hada kawunan ‘yan adawa ne kawai za su iya kifar da APC. Wannan jayayya ta samu karbuwa yayin da rikicin cikin gida na PDP ya zurfafa, wanda ya sanya ya zama kalubale ga jam’iyyar.

A farkon shekarar 2025, Atiku ya kara karfin kira ga hadin kai mai fadi, yana nunawa a matsayin zabi na karshe mai ma’ana ga ‘yan adawa. Zuwa watan Yuli, wadannan kokarin sun kai ga amincewa ta hannun ADC a matsayin hadakar jam’iyyar adawa.

Jam’iyyar ta hada manyan ‘yan siyasa da dama, ciki har da Atiku da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da tsofaffin gwamnonin jihohi Ribas da Osun da Kaduna, Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark da tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, da sauransu.

A lokacin gabatar da jam’iyyar a hukumace a Abuja, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark an nada shi a matsayin shugaban jam’iyyar na wucin gadi, tare da nada Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa na wucin gadi. Daga baya an amince da nadinsu daga kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar.

Mark ya ce jam’iyyar hadikar ta samu ne saboda bukatar dakatar da abin da ya kwatanta a matsayin “jawowar mulki na kama-karya” a Nijeriya, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da raunana cibiyoyin dimokuradiyya da jan kasar zuwa mulkin jam’iyya daya. Ya yi gargadi cewa dimokuradiyya da hadin kan kasa suna cikin hadari kuma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya daga kowane fanni na al’umma su shiga wannan lamari.

Duk da rikice-rikice a tsakanin wasu tsofaffin mambobin ADC, shugabannin kawancen suna jaddada cewa jam’iyyar tana bai wa ‘yan adawa sabon babi yayin da ake shirin zaben 2027. Duk da haka, Peter Obi na ci gaba da kasa shiga ADC a hukumance, yayin da yake da burin samun tikitin takarar shugaban kasa a 2027, ya bayyana a matsayin babban rashi a cikin kawancen. Burin Atiku Abubakar kamar dais aura masu ruwa da tsaki shi ne, muhimmanci kafafa karfin kawancen na ci gaba da hade kai, yayin da masu lura da al’amura da dama ke cewa yadda wadannan maza biyu za su tafiyar da burinsu na takarar shugaban kasa na iya tarwatsa hadewar kawancen kafin 2027.

PDP, Daga Rinjaye Zuwa Rikici

Babu wanta jam’iyya da ta fi bayyana raguwar adawa irin PDP. A lokacin karfin siyasa a Nijeriya, jam’iyyar da ta yi mulki na tsawon shekaru 16 yanzu tana gwagwarmaya don samun muhimmanci da hadin kai. A shekarar 2025, ta fuskanci mafi girman kunar bakin ciki wanda har yanzu ba ta fita a cikinsa ba, ta kara fadawa rikicin siyasa, inda APC mai mulki da sabuwar jam’iyyar adawa ta ADC ke ci gaba da amfana da sauya sheka na ‘ya’yan jam’iyyar PDP.

Tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Bincent Ogbulafor, ya taba yin alfahari cewa PDP za ta yi mulkin Nijeriya na tsawon shekaru 60. Yau, jam’iyyar na kokarin rike gwamnonin guda hudu kawai, bayan ta rasa guda bakwai cikin shekarar 2025.

Masana harkokin siyasa sun fi danganta rikicin jam’iyyar da matsalolin da suka biyo bayan zaben 2023, musamman rashin mutunta tsarin karba-karba wajen bayar da tikitin takarar shugaban kasa. Bayan shekaru takwas na Shugaba Muhammadu Buhari daga Arewacin kasar, da yawa sun yi tsammanin PDP za ta zabi dan takara daga kudu. Amma dai, kwamitin da gwamnan Jihar Benuwai a wancan lokacin, Samuel Ortom, ya jagoranta ya bayyana tikitin a bude, abin da ya janyo zazzafar muhawara mai tsanani tsakanin Atiku Abubakar da gwamnan Jihar Ribas a wancan lokacin, Nyesom Wike.

Rashin samun tikitin Wike da kin zabensa da Atiku ya ki yi a matsayin mataimaki ya raba kan jam’iyyar, ya haifar da sauya sheka da ruguza tsare-tsare daban-daban da kuma rashin jituwa wanda har yanzu an kasa warware lamarin.

Sakataren yada labarai na kasa na PDP, Kwamared Ini Ememobong, ya shaida wa manema labarai cewa yayin da jam’iyyar ke amincewa da kurakuran da aka yi a baya, shugabannin jam’iyyar a yanzu suna mai da hankali ne kan sake gina jam’iyyar.

“Ba mu yi uzuri ba wajen kirkirar sabon kwamiti gudanarwa na kasa na jam’iyyar. Mu shugabanni ne mai samar da mafita,” in ji shi.

Ya kara da cewa PDP ta kuduri aniyar sake daukar matakin farfadowa kan rawar da ta taka a matsayin babbar jam’iyyar adawa, duk da cewa wannan matsayi yana kara dusashewa daga jam’iyyar hadaka ta ADC.

Rikicin cikin PDP ya haifar da yawaitar sauya sheka. Gwamnonin irinsu Sheriff Oborebwori (Delta), Umo Eno (Akwa Ibom), Siminalayi Fubara (Ribas), Peter Mbah (Inugu), Kefas Agbu (Taraba), Caleb Mutfwang (Filato) da Ademola Adeleke (Osun) duk sun bar jam’iyyar.

Yayin da Adeleke ya shiga jam’iyyar Accord, saura sun koma APC, abin da ya tayar da fargaba na yiwuwar komawa tsarin jam’iyya daya. Yawancin wadanda suka sauya sheka su ne gwamnonin zangon farko da ke neman sake zabensu, kuma masu ruwa da tsaki suna cewa damuwar rarrabuwar ciki a PDP ta yi tasiri sosai kan shawarar da suka yanke.

Wani babban jigo a jam’iyyar PDP, wanda ya yi magana a karkashin sharadin rashin bayyana sunansa, ya ba da shawarar cewa wasu masu barin jam’iyya na iya dawowa bayan samun zangon mulki na biyu. Ya ce shugaban kasa na son zangon mulki na biyu, yayi da gwamnonin kuma na son yinn tazarce.

Ita Ma Jam’iyyar LP Na Ci Gaba Da Fama Da Rikicin Shugabaci

Jam’iyyar LP, wadda ta samu shahara a kasar nan sakamakon gwagwarmayar neman shugaban kasa na Peter Obi a shekarar 2023, ta kuma fuskanci lokaci mai cike da rudani a shekarar 2025.

Abin da ya fara faruwa matsayin rikici daga tushe ya sauya cikin sauri zuwa rarrabuwan kai a tsakani shugabannin zartarwa da shari’o’i masu tsawo a kotu da rikice-rikice kan mallakar jam’iyya wadada suke hana yanke wani hukunci a jam’iyyar. Rikicin ya raunana kwamitin dokoki na LP, ya rage kuzarin matasa, kuma ya sanya mawuyacin hali wajen komawa kyakkyawar turba kamar irin na zaben 2023, wadda jam’iyyar za ta zama mai dorewa.

Wasu jami’an da aka zaba sun duaga gum da bakinsu, yayin da wasu suka bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC, suna karfafa ra’ayin cewa LP, kadai ba za ta iya warware kalubalen kasar nan ba.

Rikicin NNPP Ta Su Kwankwaso Na Kara Kazanta

NNPP, wanda ta yi tasiri sakamakon Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ita na fama da rikicin shugabanci. Bayan saman gagarumin nasara a Kano a zaben 2023, rashin jituwa a cikin jam’iyyar ya kara kamari a 2025.

Jam’iyyar ta yi kokari wajen fadada matsayita a daukaci jihohin Nijeriya, yayin da sauya sheka da tattaunawa na hadin gwiwa da APC da ADC suka bayyana rashin tabbas a kan dogon tafiyar jam’iyyar. Lissafin siyasar Kwankwaso, ko zai ci gaba da rike iko a NNPP ko hada kai da babban jam’iyya ya bar jam’iyyar cikin rashin tabbas.

SDP, wanda wasu suka dade suna ganinta a matsayin wata dama ga ‘yan siyasa masu rashin jin dadi, na daga cikin batutuwa da suka ci wa ‘yan adawa tuwo a kwarya a 2025. Rikice-rikicen shugabanci da rashin jagora na kasa na daga ciki batutuwa da suka kawowa jam’iyyar cikas a 2025.

Ko da yake jam’iyyar ta jawo hankalin ‘yan siyasa daga lokaci zuwa lokaci wadanda ke neman jam’iyyar da za su shiga, amma ta kasa samun ci gaba mai dorewa.

ADC Da Alkawarin Da Ta Yi A 2026

Yayin da ake shiga shekarar 2026, hadakar jam’iyyar ADC ta yi alkawari zama zakarar gwajin dafi na adawa mafi tsari mai girma. Sannan ta yi alkawarin fatattakar jam’iyyar APC a kan karagar mulkin Nijeriya a 2027.

Masana harkokin siyasa na nuna shakku game da dorewar jam’iyyun adawa sakamako rashin warware rikice-rikicen cikin gida. Sun nuna cewa lallai jam’iyyun adawa a Nijeriya sun fuskace mawuyaci hali a shekarar 2025.

A cewar masanan, 2025 ta kasace mai matukar wahala ga jam’iyyu adawan Nijeriya, wanda was uke bayyana cewa tui ma kasar ta koma tsari jam’iyya guda daya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *