Barau ya ziyarci sansanin sojoji, ya nemi su kawo ƙarshen ’yan bindiga a Kano

[ad_1]



Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ziyarci sansanin jami’an tsaro a wasu sassan Kano ta Arewa, inda ya buƙaci dakarun su fatattaki ’yan bindigar da suka addabi al’umm

Ziyarar da ya kai a ranar Lahadi, ta biyo bayan hare-haren da aka kai wa wasu yankuna a ƙananan hukumomin Gwarzo, Shanono da Tsanyawa.

Hakan ne ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura sojoji, ’yan sanda da jami’an NSCDC zuwa yankunan.

Sanata Barau ya isa Kano da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Lahadi, inda ya fara da ziyartar sansanin sojoji a Unguwar Lakwaya da ke Gwarzo.

Ya gana da jami’an tsaron tare da tattaunawa da su.

Ya yaba wa jami’an tsaro kan ƙoƙarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da gode wa Shugaban Ƙasa bisa ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ya buƙaci jami’an tsaro su ci gaba da fatattakar ’yan bindiga har su kawar da su gaba ɗaya daga yankin, sannan ya roƙi al’umma su bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Haka kuma, Barau ya ziyarci wasu sansanin sojoji a Shanono da Tsanyawa, inda ya gana da shugabannin al’umma da suka nuna godiya bisa tura jami’an tsaro da kuma wasu ayyukan raya ƙasa.

Sanata Barau, ya ce ziyararsa na da nufin ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro da kuma sauraron matsalolin al’umma.

Ya kuma bayyana cewa za a gina madatsar ruwa a yankin.

Ya samu rakiyar wasu manyan ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki daga Kano ta Arewa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *