ASUU: Malaman Jami’ar FUK sun yi zanga-Zanga kan rashin cika musu alƙawura

[ad_1]



Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba.

Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar.

Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022.

Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru.

Ya ja hankalin gwamnati cewa hakan na iya haifar da damuwa a harkar ilimi a jami’ar.

Wani malami, Dakta Muhammad Sheriff Ramadan, ya ce ƙarancin albashi na tilasta wa malamai yin wasu ayyuka don samun ƙarin kuɗin shiga.

Ya buƙaci gwamnati ta ƙara albashi domin inganta rayuwarsu da harkar ilimi.

Wasu ɗaliban jami’ar, Dung Hannatu Yakubu da Precious Moses Ayomide, sun bayyana fargabarsu cewa rashin jituwar ASUU da gwamnati na iya jawo tsaikon karatu da kuma ƙara musu shekaru kafin kammala karatunsu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *