Ana zargin jami’in NYSC da sanadiyar mutuwar ’yar bautar ƙasa wajen zubar da ciki
[ad_1]
An gurfanar da wani jami’in Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), Abbas Olalekan, a gaban wata kotun majistare ta Isabo da ke Abeokuta a Jihar Ogun.
Aminiya ta ruwaito cewa, an gurfanar da jami’in ne kan zargin hannu a yunƙurin zubar da juna biyun da ya haddasa mutuwar wata ‘yar bautar ƙasa.
Wanda ake zargin, da ke kula da masu bautar ƙasa a ƙaramar hukumar Abeokuta South a Jihar Ogun wato LGI, ya musanta duk tuhume-tuhumen guda biyu da ake yi masa lokacin da aka gabatar da shi a kotu ranar Litinin.
Ana dai tuhumar jami’in ne bayan mutuwar wata ‘yar bautar ƙasa, Victoria Ariyo, wadda ake zargin ta rasu sakamakon matsalolin da ta fuskanta bayan an yi yunƙurin zubar mata da juna biyun da take ɗauke da shi.
Jami’in ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Insfeta Lawrence Olu-Balogun, ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ya haɗa baki da wasu da har yanzu ba a kai ga cafke su ba wajen aikata laifin, waɗanda ake zargin da hannunsu wajen bai wa marigayiyar magungunan zubar da ciki.
A cewarsa, lamarin ya faru ne tsakanin watan Janairu zuwa Maris a yankin Ikereku na Abeokuta, inda ya ce ana zargin akwai alaƙa ta soyayya tsakanin wanda ake tuhuma da marigayiyar, lamarin da ya kai ga ta samu juna biyu.
Sai dai lauyan wanda ake zargin, Misis Bunmi Adelabu, ta roƙi kotun da ta bayar da belinsa, tana mai kafa hujjar cewa tuhumar ba ta nuna cewa shi ne ya haddasa mutuwar marigayiyar kai tsaye ba.
Mai Shari’a A.K. Araba wadda ta jagoranci zaman kotun, ta amince da buƙatar beli kan kuɗi N500,000 tare gindaya sharuɗɗa biyu, ciki har da samar da masu tsaya masa guda biyu, kuma dole ɗaya ɗan uwansa na jini, ɗaya kuma mai aikin yi.
Kotun ta kuma umurci wanda ake zargin ya ci gaba da zama a gidan gyaran hali na Ibara har sai ya cika sharuɗɗan belin, sannan ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga Afrilu domin ci gaba da shari’a.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link