An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba.
Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi.
Uwargidan Gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta ƙaddamar da shirin a hukumance, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganin kowane yaro ya samu damar karatu.
A cewarta, shirin zai taimaka wajen fitar da dubban yara daga zaman ƙangin zaman kashe wando, tare da samar musu da makoma mai kyau ta hanyar ilimi.
An shirya aiwatar da wannan tsari a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar, inda aka tsara cewa kowacce ƙaramar hukuma za ta yi rajistar aƙalla yara 20,000, tare da raba musu kayan makaranta kyauta kamar jakunkuna, litattafai da kayan rubutu.
Aminiya ta ruwaito cewa shirin wani hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Gombe, SUBEB, UBEC da kuma UNICEF, inda ake sa ran za a rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta kafin shekarar 2030.
Da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Uwargidan Gwamna ta buƙaci iyaye da su rungumi wannan dama da hannu biyu-biyu, tana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bunƙasa ilimi da kyautata rayuwar yara a jihar.
Shugaban hukumar SUBEB, Alhaji Babaji Babadidi, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka ƙwarai wajen ƙarfafa shigar yara makaranta, tare da tabbatar da cewa ba wai kawai suna shiga ba ne, har ma suna kammala karatunsu cikin nasara.
Ita kuwa Kwamishinar Ilimi ta jihar, Farfesa Aishatu Umar Maigari, ta bayyana cewa wannan mataki babbar dama ce ta rage gibin ilimi da ke tsakanin yara maza da mata, musamman a yankunan karkara.
“Muna sa ran wannan tsari zai canza akalar rayuwar dubban yara, tare da samar da ci gaba mai ɗorewa a ɓangaren ilimi,“ in ji ta.

Mai dangantaka
[ad_2]
Source link