An kashe manomi kan taƙaddama da makiyaya a Yobe

[ad_1]



An kashe wani manomi, Muhamamad Abdullahi, mai shekara 50, daga Garin Mallam cikin ƙaramar hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe bayan an harbe shi da kibiya a lokacin wata taƙaddama da makiyaya a gonarsa.

Majiyoyi sun ce, waɗanda ake zargin, waɗanda aka bayyana a matsayin Usmanu Alhaji Musa, Buba Alhaji Manu da Ahmadu Inusa, dukkansu daga yankin Tarja Fulani cikin ƙaramar hukumar Jakusko, ana zargin sun kutsa kai cikin gonar Abdullahi.

Lokacin da manomin ya yi musu gargaɗi, nan da nan waɗanda ake zargin suka kai masa hari a wajen da harbinsa da kibiya, inda suka barshi da raunuka masu tsanani a ranar Litinin.

A ramuwar gayya da ta biyo baya, wasu mazauna ƙauyen sun kai wa Ahmadu Inusa hari, wanda ya samu raunuka a sassa daban-daban na jikinsa yadda aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibitin musamman da ke garin Gashuwa a ƙaramar hukumar Bade, inda aka tabbatar da cewa Abdullahi ya mutu, yayin da Inusa ya sami kulawar likita kuma yana kwance a asibitin.

Majiyar ta ce, tunin an miƙa gawar Abdullahi ga iyalansa don binne shi bisa ga shari’ar musulunci.

Ana ci gaba da bincike kan lamarin dangane da yanayin da ke tattare da rikicin.

Da Aminiya ke tuntuɓar kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe SP Dungus Abdulkareem ya tabbatar da labarin hakan tare da ƙarin haske da cewar lalle taƙaddama akan gona ne har ya kai ga harbin marigayi Abdullahi, kuma tuni suna tattaro waɗanda abin ya shafa da waɗanda suka aikata laifin a nan hedikwatar ‘yan sandan da ke Damaturu don ci gaba da bincike, da zarar an kammala bincike za a miƙa su ga alƙali don girbar abin da suka shuka.

A cewarsa rundunar na kiran makiyaya da manoma da su zauna lafiya da juna yayin da su makiya su guji shiga gonakin manoma don cinye musu amfanin gonakin su don tafka ta’adin da zai kai ga faɗawa cikin mummunan yanayin, haka nan su ma manoman su kaucewa noma akan hanyoyin da makiyaya ke bi ko kuma wuraren kiwon su.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *