An Karrama Karamar Hukumar Soba Da Lambar Yabo Kan Yin Fice A Aikin Noma

[ad_1]


An bayyana Karamar Hukumar Soba da ke Jihar Kaduna, a matsayin karamar hukumar da ta yi fice a fannin aikin noma.

Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci ta Tarayya ce ta ayyana Soban,  bisa gudunmawar da ta ce tana ci gaba da bayarwa wajen yin noma da bunkasa fannin, musamman a karkara.

Majalisar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci ta Kasa (NCAFS) ce ta karramar Soban da lambar yabo a taronta karo na 47 da ya gudana a Jihar Kaduna.

A cewar Majalisar Soba, ta samu gagarumin ci gaba a bangaren habaka fannin aikin noma tare kuma da tallafawa wajen samar da wadataccen abinci a jihar da kuma kasa baki-daya.

Da yake yin bayani a kan wannan lambar yabo, Shugaban Karamar Hukumar Soba, Hon. Muhammad Lawal Shehu Molash, ya sadaukar da lambar yabon ga Gwamnan Jihar Sanata Uba Sani, musamman saboda samar da tsare-tsare da kuma shirye-shiyen aikin noma a Soba.

Ya bayyana cewa, rabar da takin noma kyauta da gwamnan ya yi ga manoman jihar da magungunan feshi da taraktocin noma da sauransu, hakan ya taimaka wajen kara bunkasa fannin tare  kuma da kara karfafa guiwar kananan manoma da ke jihar.

Shehu ya kuma tabbatar da kudurin gwamnatinsa na kara samar da sauye-sauye, domin kara fadada aikin noma a Soba tare da kara samar da kayan aikin noma na zamani, musamman domin kara samar da wadataccen abinci a karkara da kuma kasa baki-daya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *