An ji ƙarar harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Guinea

[ad_1]



An ji ƙarar harbe-harben bindiga a kusa da fadar shugaban ƙasar Guinea wadda ta karaɗe kewayen babban gidan yarin ƙasar da ke yankin Kaloum na Conakry, babban birnin ƙasar.

Wasu da ke maƙwabtaka da kurkukun sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa sun fara jin harbe-harben ne da ƙarfe 9 na safiyar Talata, daga nan aka ci gaba da luguden wutar harsasai har tsawon sa’a guda.

Tuni motocin silke na ’yan sanda da jami’an tsaro na musamman suka kafa shinge a kan hanyar zuwa kurkukun, kuma zuwa wannan lokaci babu wani ƙarin bayanin abin da ke faruwa daga mahukuntan ƙasar.

Abdouramane Doukoure, wani tsohon ma’aikacin gwamnati, ya shaida wa Al-Jazeera cewa ya ji ƙarar harbe-harben a lokacin da yake wucewa ta kusa da gidan yari a cikin mota.

“Saboda cunkoson ababen hawa, kowa ya riƙa ranta a na kare domin tsira,” in ji shi.

Wani mazaunin yankin da gidansa ke kusa da gidan yarin ya ce ya ji ƙarar harbe-harbe daga cikin harabar gidan yarin, amma ya ƙara da cewa “a halin yanzu, al’amura sun lafa.”

Tashin-tashin a babban gidan yarin da ke tsakiyar Guinea ba baƙun lamari ba ne kamar yadda alƙaluma suka tabbatar.

Ko a shekarar 2023, sai da mutane tara suka rasa rayukansu a yayin wani yunƙuri na fasa gidan yari, inda wasu ’yan bindiga suka samu nasarar fitar da tsohon Shugaban Ƙasa, Moussa Dadis Camara.j


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *