AFCON 2025: Mai masaukin baƙi ta lallasa Comoros
[ad_1]
Ƙasar Maroko wadda ita ce mai masaukin baƙi a Gasar Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025, ta fara da ƙafar dama bayan lallasa Comoros da ci biyu da nema.
An take wasan da misalin ƙarfe 8 na daren ranar Lahadi a filin wasa na Mouley Abdellah da ke Birnin Rabat.
Brahim Diaz ne ya fara saka Maroko a gaba, bayan zura mata ƙwallo a minti na 55, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
A minti na 74 kuma ɗan wasan gaban Maroko, El Kaabi, ya jefa ƙwallo mai ban mamaki.
Tun farkon fara wasan Maroko ce ta mamaye filin, inda ta dinga kai hare-hare ragar Comoros.
Yanzu haka dai Maroko ce ke jan ragamar rukunin A, da maki 3 yayin da Mali da Zambiya za su ɓarje gumi a ranar Litinin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link