AFCON 2025: Dalilin Da Ya Sa Super Eagles Ba Ta Jira Bikin Karɓar Kyautar Tagulla Ba – NFF
[ad_1]
Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF), Ibrahim Gusau, ya fayyace dalilin da ya sa ‘yan wasan Super Eagles ba su halarci bikin bayar da lambobin yabo ba a wasan karshe na Gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2025 da aka kammala a ranar Lahadi.
Nijeriya ta ƙare a matsayi na uku a ranar Asabar bayan ta doke kasar Masar da ci 4-2 a bugun fenariti, duk da haka, ‘yan wasan ba su halarci bikin bayar da kyautuka da aka shirya jim kadan bayan kammala wasan Morocco da Senegal ba, duk da cewar su ma zasu karɓi kyautukan Azurfa a matsayinsu na waɗanda suka ƙare a matsayi na 3.
Da yake magana kan batun, Gusau ya bayyana cewa an tilasta wa ‘yan wasansu barin garin bayan kammala wasan saboda matsin lamba da suke samu daga kungiyoyin da suke taka leda a kasashen Turai, waɗanda suka nemi a dawo da su cikin gaggawa, shugaban na NFF ya kara da cewa ba iya ‘yan Nijeriya kawai lamarin ya shafa ba har da kasar Masar da suka buga wasa tsakaninta da Nijeriya.
“Yanzu haka kyautukan na hannuna domin raba masu, haka abin yake ba a iya Nijeriya ba har da kasar Masar” inji Gusau a wani rubutu da ya yi a shafin X, wannan ne karo na 9 da Nijeriya ke karewa a matsayi na 3 a gasar AFCON, inda ta ci gaba da zama a matsayin kasar da tafi karewa a matsayi na 3 a tarihin gasar.
[ad_2]
Source link