Duniya Ta Shaida Kokarin Sin Bisa Shirin Ci Gaban Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’Umma Na Shekaru Biyar-Biyar Karo Na 15
[ad_1]
An kammala taron majalisar NPC da CPPCC na 2026 cikin nasara, inda aka zartar da muhimman takardu, kamar na tsarin shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15, matakin da ya tabbatar da shirin a sabon zagaye. Wadannan manyan taruka 2 na Sin, ba wai kawai sun tanadi tsara aikin da Sin za ta aiwatar a nan gaba ba ne, har ma sun samar da alkibla ta samun wadata tare ga kasashen duniya, kuma kafofin yada labarai na kasa da kasa sun yaba da hakan sosai.
Sin na amfani da shirin na shakaru biyar-biyar don rike makomarta mai kyau ta dogaro da karfin kai, tana kuma nacewa cikakken jagorancin jam’iyyar JKS, da tsare-tsare daga manyan fannoni a bangaren kimiyya, da mayar da kwarewar tsare-tsare zuwa doka, kana tana nuna fa’idodin tsari na tattara karfin kowa da kowa don gudanar da manyan ayyuka, wannan shi ne sirrin nasarar “tsarin Sin”.
Har ila yau, Sin na mai da hankali kan samun ingantaccen ci gaba, tana kula da daidaiton karuwar adadi da ingancin ci gaba, kuma tana bunkasa sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, da kafa sabbin siffofin tattalin arziki na hikima, da kuma gaggauta karkata zuwa hanyar samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba bisa dokar kare muhalli, da kuma gaggauta ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Sin na ci gaba da inganta rayuwar jama’a, da mai da moriyar jama’a a gaban komai. Abubuwan dake shafar rayuwar jama’a a shirin karo na 15 ya wuce sulusi, wadanda suke mai da hankali kan kare lafiyar jama’a, da inganta tsarin inshorar zamantakewa da kiwon lafiya, da kuma inganta rayuwar jama’a.
Sin na nacewa ga bude kofa da juriya, da samar da fa’idodin babbar kasuwa, da fadada bude kofa bisa manufofin kasa da kasa, ta yadda babbar kasuwar Sin za ta ci gaba da samar da damammaki ga duniya. Sin na tsayawa tsayin daka kan kare ra’ayin gudanar da harkokin duniya tsakanin mabambantan bangarori, da gaggauta gina kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya, wanda hakan ya sa ta zama amintaccen karfi mai inganci ga kwanciyar hankalin duniya. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link