Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Wajen Haƙar Ma’adanai A Filato Bayan Mutuwar Mutane 35

[ad_1]

Gwamnatin Tarayya ta umarci a rufe wani ramin haƙar ma’adanai a Jihar Filato bayan wasu ma’aikata 35 sun mutu sakamakon shaƙar hayaƙin guba.

Lamarin ya faru a ƙaramar hukumar Wase, kuma wajen mallakin kamfanin Solid Unit Nigeria Limited ne.

  • DSS Ta Kama El-Rufai Bayan EFCC Ta Bayar Da Belinsa
  • Nazarin CGTN: Barkwancin “Zama Basine” Ya Rikide Zuwa Buri Na Zahiri

An ruwaito cewa mutanen garin da ke hƙko ma’adanai a wajen ba su san hayaƙin na da hatsari ba.

Dele Alake, Ministan Ci Gaban Ma’adanai, ya aike da ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar da iyalan waɗanda abin ya shafa.

Haka kuma ya tura ƙwararru, ciki har da masana harkar ma’adanai da tsare muhalli, domin yin bincike kan abin da ya faru.

Rahotanni sun nuna cewa kamfanin ya ba da izinin hako ma’adanai ga mutanen garin saboda yadda mutane ke neman aikin yi.

Mutane da yawa waɗanda lamarin ya shafa a kai asibitoci, amma har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka tsallake rijiya da baya ba.

Ministan ya yi alƙawarin yin ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da bincike.

Jami’an sun yi gargaɗin cewa rashin tsaro a wajen haƙar ma’adanai babbar matsala ce.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *