Babandede ya sabunta rajistarsa a APC

[ad_1]



Tsohon Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya sabunta rajistar zamansa dan jam’iyyar APC a Hadejia, Jihar Jigawa.

Babandede ya samu gagarumar tarba daga dimbin magoya baya da suka tarbe shi daga ƙofar gari har zuwa mazabarsa ta Kasuwar Kuda. Tafiyar mintuna kadan ce, amana ta ɗauki sama da awa hudu saboda yawan jama’ar da suka fito.

Muhammad Babandede ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Danmodi, tare da tabbatar da goyon bayansa ga su da jam’iyyar APC.

Dattijo kuma gogaggen dan siyasa Ambasada Haruna Ginsau da Shugabannin Jam’iyyar APC sun yaba masa kan biyayya da sadaukarwa ga jam’iyya.

Abin da aka tsara ya dauki yan mintuna ya ɗauki sama da awa huɗu saboda yawan jama’a daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa, musamman mazaɓar sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *