Mu’amala Tsakanin Shugabannin Sin Da Amurka Tana Taka Muhimmiyar Rawa A Dangantakar Kasashen


Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian, ya ce mu’amala tsakanin shugabannin Sin da Amurka tana taka muhimmiyar rawa a dangantakar kasashen. Ya kara da cewa a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi kwanan nan tsakanin shugabannin kasashen biyu, shugaba Trump ya nanata aniyarsa ta ziyartar Sin a watan Afrilu, kuma shugaba Xi Jinping ya nanata gayyatar da ya yi wa shugaba Trump ta ziyartar Sin, kuma bangarorin biyu sun ci gaba da tattaunawa kan wannan batu.

Lin ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum da aka gudanar yau Alhamis.

Dangane da batutuwan da suka shafi kamfanin Nexperia, Lin Jian ya ce ya kamata Netherlands ta samar da yanayi mai kyau don kiyaye kwanciyar hankali ga tsarin samar da kayayyakin semiconductor ta duniya. Kuma Sin za ta ci gaba da tallafawa kamfanoninta wajen kare hakkoki da muradunsu na halal.

Bugu da kari, a martanin da ya mayar game da halin da ake ciki a zirin Gaza, Lin Jian ya bayyana cewa, Gaza da yammacin bakin kogin Jordan dukkansu yankunan Falasdinu ne da ba za a iya raba su daga kasar ba, kuma shirin kafa “kasashe biyu” babbar hanya ce ta warware matsalar Falasdinu. (Safiyah Ma)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *