An Shirya Bikin Share Fagen Shirin Talibijin Na CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar Gargajiyar Kasar Sin A Kasashen Rasha da Faransa Da Brasil Da Kuma Koriya Ta Kudu
[ad_1]
An gudanar da bikin share fagen shirin talibijin na CMG na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin mai taken “Duniya tana kallon shirin na CMG tare” a ranar 10 ga watan Fabrairu a Moscow na kasar Rasha. An shirya bikin ne bisa hadin gwiwar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG), da jami’ar sada zumunci tsakanin al’ummu ta kasar Rasha.
Babban daraktan CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce, a matsayin shirin al’adu mafi yawan masu kallo a duniya, an riga an gudanar da shirin talibijin na CMG na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a cikin shekaru 43 da suka gabata a jere, wanda ya kyautata zumunci a tsakanin Sinawa a duniya da abokansu a jajibirin bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. A bara CMG ta hada kai da kafofin yada labaru fiye da 3100 a duniya wajen watsa labaru kan shirin don kasashen duniya su kara fahimtar bikin Bazara na kasar Sin. A bana kuma, an yi wa bikin taken “Ba za a iya tsayar da gudun dawaki ba”, inda za a yi amfani da sabbin fasahohin “5G+4K/8K+AI”, da fifikon da CMG yake da shi na yada shirye-shirye da harsuna 85, don samar da wani gaggarumin bikin al’adu ga masu kallo na cikin gida da waje.
Bugu da kari, a ranar 10 ga wata, an nuna bidiyon a Brasilia na kasar Brazil, kuma ran nan an nuna shi a gun bikin murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa da aka yi a hedkwatar hukumar bunkasa ilmi, kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO dake birnin Paris, fadar mulkin kasar Faransa. Kuma, a ranar 11 ga wata, an nuna shi a liyafar maraba da bikin bazara na ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Koriya ta Kudu. (Tasallah Yuan, Maryam Yang)
[ad_2]
Source link