Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Hukumar Alhazai Ta Ƙasa Ambasada Ismail Abba Yusuf
Ambasada Ismail Abba Yusuf tsohon jami’in diflomasiyya ne da ya shafe sama da shekaru 35 yana hidima a Ma’aikatar Harkokin ƙasashen Waje ta Nijeriya, tare da gogewa mai zurfi a harkokin gudanar da aikin Hajji da ayyukan gwamnati. An haife shi ranar 7 ga Yuli, 1962 a Mubi, Jihar Adamawa, kuma ya kammala digiri a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto a 1985.
Ya shiga aikin diflomasiyya a Disambar 1986 bayan kammala NYSC, inda ya yi aiki a ofisoshin jakadancin Nijeriya a ƙasashen Argentina, Italiya da China. A shalƙwatar ma’aikatar kuwa, ya yi aiki a sassa daban-daban da suka haɗa da nazari, da ayyuka, da horaswa, da gudanarwa da kula da harkokin alhazai.
- Tinubu Ya Naɗa Sabon Shugaban NAHCON
- Shugaban Hukumar NAHCON Ya Yi Murabus Bayan Ƙorafe-ƙorafe A Kansa
Tsakanin 2002 zuwa 2007, ya jagoranci sakatariyar Kwamitocin Shugaban Ƙasa kan Hajji, wanda aikinsa ya taimaka wajen shimfiɗa tubalin kafa NAHCON a 2006, inda ya kuma yi aiki a matsayin Sakatare na Tsare-tsare. Haka kuma ya kasance sakatare ga tawagogin Gwamnatin Tarayya (Amirul Hajj) a shekarun 2012 da 2013, tare da taka muhimmiyar rawa wajen ƙirƙiro tsarin Hajj Savings Scheme bayan wata tawaga ta kai ziyara Malaysia da Indonesia a 2005 domin nazarin tsarin hajjin ƙasashen.
Ya kai matsayin Darakta a 2013, sannan a 2021 aka naɗa shi Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Turkiyya, inda ya taka rawa wajen ƙarfafa dangantaka a fannonin tsaro, kasuwanci da masana’antu. Yana jin Hausa, da Yoruba, da Igala, da Turanci da Sifaniyanci, kuma ana sa ran zai kawo ƙwarewa da gogewa mai zurfi a sabon matsayinsa na Shugaban NAHCON.