Real Madrid da UEFA sun cimma matsaya kan gasar Super League
[ad_1]
Real Madrid da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Turai (UEFA) sun sanar da cimma yarjejeniya domin kawo ƙarshen rikicin shari’a da ya biyo bayan rushewar gasar European Super League.
Madrid, wadda shugabanta Florentino Perez ya daɗe yana goyon bayan gasar, tare da kamfanin A22 Sports Management, sun nemi dala biliyan 4 a matsayin diyya daga UEFA bayan rushewar shirin.
Sanarwar ta ce ɓangarorin sun amince kan mutunta tsare-tsaren wasanni da ɗorewar ƙungiyoyi ƙwallon ƙafa na tsawon lokaci, tare da inganta ƙwarewar magoya baya ta hanyar fasaha.
Wata majiya ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “mai tarihi” wadda za ta buɗe sabon babin sulhu a harkar ƙwallon Turai.
A makon jiya ne Barcelona ta janye daga shirin, bayan da yawancin kulob ɗin Turai 12 da suka ƙaddamar da gasar a 2021 suka janye sakamakon matsin lambar magoya baya da hukumomi.
Tun dai bayan dakatar da shirye-shirye soma gasar ce ƙungiyoyi ƙwallon ƙafa shida na Ingila da suka nuna sha’awa a karon farko suka janye da suka haɗa da Manchester City, Arsenal, Liverpool, Manchester United, Tottenham da Chelsea.
Sauran kulob-kulob ɗin da su ma suka biyo sahu a shekarar 2024 sun haɗa da Atletico Madrid, Inter Milan, AC Milan da Juventus, lamarin da ya rage Barcelona da Madrid kaɗai a shari’ar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link