Ba Za Mu Aminta Da Hare-haren ‘Yan Bindiga Ba, Dole A Kawo Ƙarshensu — Tinubu

[ad_1]

Shugaba Bola Tinubu ya ce garkuwa da mutane da ta’addanci ba al’adun Nijeriya ba ne kuma dole ne a kawo ƙarshensu.

Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar matsala da ke hana ci gaban tattalin arziƙin ƙasa.

  • Kamfanin Matatar Man Fetur Na Dangote Ya Rage Farashin Mai Zuwa ₦774
  • Na Yi Murabus Ne Saboda Dalilai Na Ƙashin Kaina – Shugaban Hukumar Aikin Hajji

A lokacin taron Kwamitin Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC) da aka gudanar a Abuja, Tinubu ya yi alƙawarin ƙarfafa jami’an tsaro domin shawo kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Ya ce yaƙi da rashin tsaro ya sa shugabanni “ba sa barci,” amma ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnati za ta yi nasara.

Maganganunsa na zuwa ne biyo bayan hare-hare a jihohin Kwara da Katsina, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, yayin da aka sace wasu.

Tinubu ya yaba wa wasu gwamnonin, ciki har da na Borno da Katsina, kan ƙoƙarinsu wajen yaƙi da rashin tsaro.

Haka kuma, ya danganta wasu matsalolin tsaro da rikice-rikicen manoma da makiyaya, yana mai kira a yi sauye-sauyen fagen kiwo, ciki har da shirin gandun daji, domin rage rikici.

Shugaban ya ce gwamnatinsa na da niyyar tabbatar da nasarar kiwo da bunƙasa harkar dabbobi a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin kawo zaman lafiya da ci gaban tattalin arziƙi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *