Ofishin Jakadancin Sin A Mozambique Ya Shirya Liyafar Murnar Bikin Bazara

[ad_1]

Ofishin jakadancin Sin a Mozambique, ya gudanar da liyafar Bikin Bazara wato bikin murnar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta Sin na shekara ta 2026 a jiya 9 ga watan Fabrairu, inda aka haska bidiyon shirin yayata bikin na shekarar doki wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya tsara.

Jakadiyar Sin a Mozambique Zheng Xuan ta bayyana fatan alheri na bikin shekarar doki ga baki mahalarta, kuma ta yi bayanin cewa, a cikin shekarar doki da ke dab da shigowa, Sin za ta fara gudanar da “shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15”, kana Sin za ta fadada bude kasuwarta ga ketare, da raba damammakinta ga kasashen duniya, ta yadda za ta ci gaba da ba da tabbaci ga zaman lafiya da bunkasar duniya.

Wakilin hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da al’adu ta MDD (UNESCO) a Mozambique Michael Croft ya ce, Bikin Bazara na Sin ba liyafar al’adu kawai ba ne, har ma yana inganta jituwa da hadewa da amincewa da kuma zaman tare, kana da hadin kai da zaman lafiya a duniya. Wannan ruhin shi ma zai bayyana sosai a cikin ayyukan “shekarar musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka” na 2026.

A cikin ‘yan kwanakin nan, tawagar Sin ta dindindin a MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Vienna da kuma ofishin jakadancin Sin a Laos da Malaysia da Jamus da kuma Argentina, kana da Morocco da sauransu, su ma sun gudanar da liyafar bikin don murnar zuwan sabuwar shekarar doki tare. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *