Majalisar Dattawa ta amince da tsarin tura sakamakon zaɓe ta intanet

[ad_1]



Majalisar Dattawa ta amince da tsarin tura sakamakon zaɓe kai-tsaye ta intanet daga rumfar zaɓe zuwa cibiyar tattara sakamakon zaɓen.

Majalisar ta amince da wannan tsari ne wanda ke cikin batun ƙudurin gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2022 bayan wani zaman gaggawa da ta gudanar a Talatar nan.

Sai dai Majalisar ta ce aika sakamakon kai-tsaye ta na’ura zai kasance matakin farko na aika sakamakon, amma idan an samu matsalar intanet, INEC za ta yi amfani da takarda a rubuce wajen aika sakamakon kamar yadda aka saba yi a baya.

Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da ƙudirin a lokacin zaman gaggawa da majalisa ta yi kan dokar, yayin da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya amince da ƙudirin bayan amincewar sauran ’yan majalisar.

Daga nan ne kuma majalisar ta kafa wani kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki da Majalisar Wakilai don tsefe dokokin kamar yadda tsarin amincewa da dokoki ya tanadar.

Tun da fari an samu saɓanin ra’ayi tsakanin Majalisar Wakilai wacce ta yarda a sanya tsarin ya zama dole, da kuma Majalisar Dattawa wacce ta dage kan cewa hakan “zaɓi ne”, ba wajibi ba.

Ana iya tuna cewa, a makon jiya ne Majalisar Dattawa ta yi watsi da tsarin tura sakamakon zaɓen kai tsaye ta intanet, lamarin da ya yamutsa hazo har aka soma zanga-zanga a wasu sassan ƙasar ciki har da Birnin Tarayya Abuja.

Sai dai bayan cimma wannan matsaya, Majalisar Dattawan ta bayyana cewa hakan zai ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwar fitowa kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓen, tare da bai wa ’yan ƙasa damar bin diddigin harkokin zaɓe cikin gaskiya kuma a bayyane.

Ana sa ran ’yan Nijeriya za su fita rumfunan zaɓe a zangon farko na shekarar 2027 domin zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni, da kuma ’yan majalisun dokoki na jiha da na tarayya.

A tsawon shekaru goma da suka gabata, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kawo tsarin amfani da fasahohin zamani da nufin ƙarfafa sahihancin gudanarwa da kuma sakamakon zaɓe.

Sai dai duk da haka, ƙoƙarin da INEC ta yi bai yi wani tasiri sosai ba, la’akari da yaddda rikice-rikicen bayan zaɓe da shari’o’i kan ƙorafe-ƙorafen zaɓen suka zama ruwan dare.

Masana na ganin amincewar jama’a ga tsarin zaɓe za ta ƙaru matuƙa idan aka tilasta wa rumfunan zaɓe 176,000 da ke faɗin ƙasar nan su riƙa wallafa sakamakonsu kai tsaye a wani shafin yanar gizo guda da kowa zai iya shiga.

Alƙaluma sun nuna cewa tsawon shekaru goma da suka gabata, yawan mutanen da ke fitowa kaɗa ƙuri’a na raguwa, sakamakon yadda da galibi suke ɗauka cewa ƙuri’unsu ba sa wani tasiri.

An samu kashi 27 cikin 100 na waɗanda suka fito kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, wanda shi ne mafi ƙanƙanta tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

A watan Mayun 2025 kuma, ’yan Majalisar Tarayya suka tilasta janye wani ƙudiri da ya tanadi hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari ko tarar naira 100,000 ga duk wanda ya cancanci zaɓe amma ya ƙi fita kaɗa ƙuri’a, bayan da jama’a suka nuna rashin amincewa da ƙudurin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *