Rikici ya kunno kai a APC a Kano bayan sauya shekar Abba
[ad_1]
Kimanin makonni biyu bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa Jam’iyyar APC a Jihar Kano, da alamar baraka ta kunno kai game da makomar sabbin shiga da tsoffin ’yan jam’iyyar.
Tun da farko masana harkokin siyasa sun yi hasashen yiwuwar rikici tsakanin ’yan APC masu burin kujerun shugabanci daban-daban bayan sauyin shekar.
Duk da cewa a wancan lokaci an dauki hasashen a matsayin zato, abubuwan da suka faru a karshen mako a wasu muhimman kananan hukumomi sun fara nuna alamun rikici.
Rahotanni daga Kananan Hukumomin Birnin Kano da Dawakin Tofa sun nuna cewa akwai sabani da ke tasowa a cikin jam’iyyar, inda aka ce manyan ’yan jam’iyya sun gudanar da taruka daban-daban kan batun yadda za a hada kan mambobi.
Aminiya ta gano cewa takaddamar tana da nasaba ne da makomar sabbin mambobin jam’iyyar da suka shigo daga NNPP tare da Gwamna Abba, da kuma mambobin da suka kasance a APC tun kafin nan.
Wannan ya kunno kai ne a daidai lokacin da Jam’iyar ke kokarin hade kan ’ya’yanta inda ta fara gudanar da taruka domin cimma hakan.
Aminiya ta gano cewa tsagin tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje ya gudanar da nasa taron inda ya samu halarcin shugaban jam’iyya na Karamar Hukumar Birni, Sani Abubakar Mai Fata Sharada da kuma Mutari Ishaq Yakasai wana ke neman takarar kujerar shugaban jam’iyyar na jihar, da kuma Baffa Babba Dan’agundi; Injiniya Sagir Koki; Hon. Salim Hashim Gwangwazo; Nura Hussain; Hon. Nabil Sarki Daneji; Hon. Ibrahim Kankarofi; Hon. Kabiru Labour; Alhaji Kabiru Rabi’u; Malam Garba Yusuf Abubakar; Hon. Aliko Shuaibu Mukhtar, da wasu kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman.
A gefe guda kuma, wasu mambobin jam’iyyar da ke goyon bayan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, sun gudanar da taro a wani wurin daban, karkashin jagorancin Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo da Malam Muhammad Ibrahim Kankarofi.
Wadanda suka halarci wannan taro sun hada da Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo (Alhajin Baba), Malam Ibrahim Kankarofi, Hamza Darma, Alhaji Faruq Iya, Fa’izu Alfindiki, Hon. Dan Bello Aminu, Uba Zubairu Yakasai, Injiniya Garba Ahmed Kofar Wambai, Hajiya Rabi Aminu Me-Mai, Hon. Nasiru Hanga, Hon. Mu’azzam Marafa, Alhaji Nasiru Uwe, Alhaji Dauda Raula da Hon. Na Balalu Mai Turare, da sauransu.
Majiyoyi sun bayyana cewa tarukan sun kasance wani bangare na shirin gudanar da babban taro na jam’iyyar, inda aka tattauna dabaru da kuma yanke matsaya kan makomar APC a jihar. Sai dai yadda bangarorin suka zabi yin taro a wurare daban-daban na nuna cewa akwai sabani da bai warware ba a cikin APC Kano.
An samu irin haka kuma a karshen mako a mazabar Dan Majalisar Tarayya ta Dawakin-Tofa/Tofa/Rimingado, ina magoya bayan masu neman takara daban-daban suka tayar da jijiyoyin wuya a lokacin taron hadin kan jam’iyya.
Majiyoyi sun ce an shirya taron ne domin karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar, amma ya rikice bayan sa-in-sa mai zafi tsakanin magoya bayan manyan ’yan siyasa. Mazabar dai na daga cikin wuraren da ake ganin za a yi takara mai zafi saboda muhimmancin siyasa da take da su.
A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, rikicin ya fara ne bayan tsohuwar shugabar mata ta NNPP a Dawakin-Tofa, Hajiya Hasiya Aminu, wadda ta sauya sheka zuwa APC, ta fito fili ta caccaki dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar, Tijjani Abdulkadir Jobe.
Hasiya ta bayyana Jobe a matsayin wanda ya gaza, tare da kira gare shi da ya yi koyi da Shugaban Karamar Hukumar Dawakin-Tofa, Anas Mukhtar Bello Dan Maliki, da Injiniya Abba Ganduje. Wannan furuci ya fusata Jobe da magoya bayansa, lamarin da ya janyo hayaniya har taron ya kare ba tare da cimma matsaya ba.
Wannan taro dai shi ne na farko da ya hada kusan dukkan manyan ’yan siyasa da masu neman mukamai a mazabar, sai dai rikicin da ya barke ya nuna akwai kalubale wajen samun daidaito a cikin APC a yankin.
Martanin APC kan zargin rikici
Sai dai kuma, magana da yawun APC a Kano, Ahmad Aruwa, ya yi watsi da zarge-zargen cewa akwai rikici a cikin jam’iyyar.
Ya ce tun bayan sauyin sheka da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi zuwa APC, mambobi na ci gaba da zama lafiya tare.
Aruwa ya bayyana cewa mai makon rikici, ’yan siyasa suna kokarin daidaita kananan sabani kafin tarukan jam’iyya.
“Tun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam’iyyarmu, muna zaune lafiya. Babu wata sabani a APC. Abin da ke faruwa al’ada ce a tsarin dimokuradiyya, inda mutane kan yi sabani kafin su cimma matsaya. Wasu kananan hukumomi kawai ne ke kammala shirye-shiryen tarukan jam’iyya,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link