Dalilin Da Ya Sa Gwamnan Bauchi Ya Sauke Kwamishinan Tsaron Cikin Gida

[ad_1]

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sauƙe Alhaji Ibrahim Gambo Galadima daga muƙaminsa na Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Kula da Harkokin Cikin Gida, inda sallamar ta fara aiki nan take.

Matakin na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce an amince da yin ƙaramin sauyi a Majalisar Zartarwa ta Jihar (SEC). Sai dai gwamnatin ba ta bayyana takamaiman dalilin sauyin ba.

  • Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Jaridan Bauchi Sun Yi Hatsari Yayin Ɗaukan Rahoton Ayyukan NEDC
  • ‘Yansanda Sun Kama Matasa 2 Kan Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Man Fetur A Bauchi

Sanarwar ta bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin kyautata shugabanci da inganta yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati, tare da sake duba tsarin majalisar kwamishinoni domin shigar da sabbin dabaru da daidaita tafiyar da ayyuka.

Gwamna Bala Mohammed ya gode wa Galadima bisa gudunmawar da ya bayar, tare da yi masa fatan alheri. Haka kuma ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci, yana mai cewa za a sanar da wanda zai maye gurbinsa nan ba da jimawa ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *