El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
[ad_1]
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ya bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban ƙasa a 2027 ko kuma ya goyi bayan wani ɗan takara. Ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da nufin ruɗar da jama’a.
El-Rufai ya ce bai taɓa yin irin wannan magana ba, a hira ko rubutu ko a shafukansa na sada zumunta. Ya jaddada cewa duk ra’ayoyinsa yana bayyana su ne kai tsaye a kafafen sada zumuntarsa da aka tantance.
Ya kuma gargaɗi ‘yan jarida da jama’a da kada su jingina masa ra’ayoyin da wasu suka rubuta, ko da kuwa ya yaɗa su domin tattaunawar ƙasa. A cewarsa, hakan ba daidai ba ne kuma yana rikita gaskiya.
A ƙarshe, El-Rufai ya yi kira da a tabbatar da labari kafin yaɗawa, yana mai cewa ya kamata a jingina masa magana ne kawai idan ya faɗe ta a fili a kafafensa na ainihi ko a hirarraki da kafafen yaɗa labarai masu sahihanci.
[ad_2]
Source link