APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a Jigawa

[ad_1]



Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar.

A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar rashin ɗa’a daga wani rukunin magoya bayan tsohon gwamna kuma Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da ta kira da suna “Badaru Boys.”

Sanarwar ta zargi wannan rukunin da haddasa rikice-rikice a wuraren tarukan siyasa, tare da yunƙurin ɓata sunan gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi.

Ta bayyana cewa hakan ya faru a wurare da dama ciki har da Majiya, Gumel da kuma zaben cike gurbin Babura/Garki, inda aka ce sun tayar da rikici.

Jam’iyyar ta kuma zargi magoya bayan tsohon gwamnan da kai hare-hare da cin fuska ga gwamnatin yanzu, musamman a taron da aka gudanar a Kafin Hausa, garin Gwamna Namadi, inda suka yi ta zage-zage.

APC ta bayyana takaicinta kan yadda tsohon gwamna bai tsawatar wa magoya bayansa ba, sai dai ta yaba wa Gwamna Namadi bisa haƙuri da natsuwa da yake nunawa duk da tayar da hankali da ake yi masa.

“Fitinar ‘Badaru Boys’ ta yi yawa. Wannan ɗabi’a, wadda za ta iya ɓata wa jam’iyya suna, ta sabawa sashe na 21 na kundin tsarin mulkin APC,” inji sanarwar.

Jam’iyyar ta yi gargaɗi cewa idan irin wannan hali ya ci gaba, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da tanade-tanaden kundin tsarin mulki domin kawo ɗa’a. Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa don hana ɓarkewar rikici daga rashin jituwar siyasa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *