Hukumar CAC ta soke lasisin kamfanoni 400,000 a Najeriya a 2025




Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Kasa (CAC) ta bayyana cewa ta cire sama da kamfanoni 400,000 daga rajistarta a shekarar 2025, saboda rashin aiki da kuma kin bin ka’idojin da aka gindaya.

Babban Sakataren Hukumar, Husseini Magaji, ya bayyana haka a lokacin zagayen wayar da kai da hukumar ta shirya a karshen mako a birnin Abuja.

Ya ce, “A shekarar 2025 kaɗai, hukumar ta soke sama da kamfanoni 400,000 daga rajistarta,” domin tsaftace bayanan da ke cikin kundin rajista daga kamfanonin da ba sa aiki ko kuma marasa bin doka.

Magaji ya ƙara da cewa wannan mataki na da nufin kare sahihancin kundin rajistar kamfanoni na ƙasa.

Ya ce, “Yau CAC na yin aiki a ko’ina, a kowane lokaci, har tsawon awanni 24 a rana. Za ka iya yin rajistar kasuwancinka daga ɗakinka ba tare da zuwa ofisoshinmu ba.”

Babban Sakataren ya kuma bayyana cewa hukumar, tare da haɗin gwiwar Hukumar Samar da Ci gaban Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i (SMEDAN), ta taimaka wajen yin rajistar kasuwanci kyauta ga ’yan kasuwa 250,000 a matsayin goyon baya ga ƙananan ’yan kasuwa.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *