Tinubu zai ziyarci Birtaniya a karon farko bayan shekaru 37
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa Birtaniya a watan Maris, kamar yadda Fadar Buckingham ta sanar.
Wannan ita ce ziyara ta farko da shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37.
Ziyara t ƙarshe da ya kai a shekarar 1989, lokacin da shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya kai ziyara inda Sarauniya Elizabeth II ta karɓe shi.
Sarkin Birtaniya, Charles III ne, ya gayyaci Shugaba Tinubu zuwa Birtaniya.
Shugaban zai tafi tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu.
Irin wannan ziyara ta aiki na taimakawa wajen ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashe.
Shugaba Tinubu da Sarki Charles duk sun hau karagar mulki a watan Mayun 2023, kuma sun gana da juna sau da dama tun bayan hawansu mulki.
A watan Nuwamban 2023, sun haɗu a Dubai yayin taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya (COP28).
Haka kuma, a watan Satumban 2024, Sarki Charles ya karɓi Shugaba Tinubu a Fadar Buckingham domin wata ganawa ta musamman.
Har yanzu Fadar Buckingham ba ta bayyana cikakken jadawalin abubuwan da za su gudana a yayin ziyarar ta ranar 18 ga watan Maris ba, amma ta ce za ta tu ƙarin bayani a nan gaba.
Sarki Charles na da kyakkyawar alaƙa da Najeriya, kuma ya taɓa bayyana cewa yana son waƙoƙin ‘Afrobeats’.
Kafin ya zama sarki, ya taɓa kawo ziyara Najeriya sau huɗu a shekarun 1990, 1999, 2006 da 2018.
A shekarar 2023, ƙungiyar King’s Trust International, wacce a da ake kira Prince’s Trust ta fara aiki a hukumance a Najeriya, inda ta ƙaddamar da shiri na tallafa wa matasa domin rage rashin aikin yi da ƙarfafa kasuwanci.