Xi Ya Taya Fernandez Murnar Lashe Zaben Shugabar Costa Rica

[ad_1]

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya taya Laura Fernandez murna kan zabenta a matsayin shugabar kasar Costa Rica. A cikin sakonsa da aka aika ranar Alhamis, Xi ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya shekaru 18 da suka gabata, Sin da Costa Rica sun samu gagarumin ci gaba a dangantakarsu, tare da samun manyan nasarori a fannonin musaya da hadin gwiwa a bangarori iriiri, lamarin da ya samar da fa’idodi na zahiri ga al’ummomin kasashen biyu.

Ya ce, kwararan hujjoji na gaskiya sun tabbatar da cewa, ci gaban dangantakar Sin da Costa Rica na cika manyan muradun kasashen biyu da al’ummominsu, tare da nuna yanayin zamani da kuma burin jama’a na bai-daya.

Xi ya kara da cewa, yana ba da muhimmanci sosai ga ci gaban alakar Sin da Costa Rica, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Fernandez domin karfafa sadarwa mai alfanu, da zurfafa amincewar siyasa, da kuma zurfafa hadin gwiwa a fannoni dabandaban, kana da kara matse kaimi wajen ganin dangantakar kasashen biyu na samun ci gaba cikin kwanciyar hankali bisa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” domin samar da karin cin moriya ga al’ummomin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *