Yadda Ake Hada Sabulu Don Gyaran Fata Da Gyaran Fuska

[ad_1]

(1) Domin kyawun fuska

Abubuwan da ake bukata:

Garin Zogale, Farar albasa, Sabulun Ghana, Sabulun Dettol, Sabulun salo

Ga Yadda Za A Hada:

Ki samu sabulun Ghana da na salo daidai kai daya, sai ki samu Dettol shi ma kamar guda biyu, sannan ki sami garin Zogale cokali biyu sai Albasa manya guda biyu duk sai ki hada su a Turmi ki kirbe su, sannan sai ki juye a roba mai murfi za ki rika wanke fuskarki da shi yana da kyau sosai yana magance kurajen fuska.

(2) Kisa

Abubuwan da za a tanada:

Dilka da sukari, Lemon tsami, Man Zogale, Turaren Du’aul jannah

Yadda za a hada:

Za ki zuba ruwa a Tukunya sai ki zuba duk kayan a ciki, sannan ki dora a wuta amma kadan za ki sa a wutar sai ki bar shi har sai ya tafasa ya yi kumfa, sannan ki sauke idan ya huce ki rika dangwala kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa, sai ki karasa murje shi sannan ki yi wanka da ruwan dumi, fatarki za ta yi kyau.

(3)Sabulu na musamman:

Abubuwan da ake bukata:

Madarar turare, lalle da Dilka, Ganyen Magarya, Kurkur, Dudu Osun da Detol, Sabulun Ghana.

Yadda za a hada:

Hada su wuri daya a daka su a Turmi mai kyau su hade jikinsu sosai sai ki ringa wanka da shi.

Ga wani hadi mai kyau da zai gyara fata ba tare da illa ba, ku jarraba amfani da shi:

Da farko za ku samo Sabulu na wanka wanda ba shi da karfin chemicals, sai ku goga shi da abin gogawa ya zama kamar gari, sannan ku samo Man Kwakwa, Zuma, Rose water, Garin darbejiya, Garin bawon lemon zaki, Coffe da Kurkur, duk ku zuba cikin wannan sabulun da kuka goga sannan ku hade shi ku juya yadda dukka zai hade, sannan ku samo Baikin soda ku sanya a ciki ku juya saboda kada ya lalace, daga nan za ku juye shi cikin mazubi da za ku yi amfani da shi.

Wannan hadin yana da kyau, yana sa fata ta yi kyau sosai ba tare da sauya yana yin fata ba in sha Allahu!

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *