An sace babban limami da wasu mutum 2 a kudancin Kaduna
’Yan bindiga sun yi garkuwa da Babban Limamin Juma’a na Janjala da ke Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, Malam Bello Abdullahi, da wani jagoran Fulani a yankin, Alhaji Shehu Bello da kuma wata mata.
A ’yan kwanakin nan, ’yan bindiga sun kutsa wasu ƙauyuka da dama a yankin, ciki har da Iddo, Gidan-Makeri, Kohoto da Janjala, inda suka yi garkuwa da mutane da dama tare da sace shanu.
Sakamakon waɗannan hare-hare, mazauna Kohoto, wani ƙauye da ke makwabtaka da Janjala, sun tsere daga gidajensu a ranar Asabar.
Wannan ya biyo bayan wa’adin kwanaki bakwai da ’yan bindiga suka bayar domin al’ummar kauyen su tara musu Naira miliyan 6 don a saki wata mata da ’ya’ya huɗu na wani ɗan sa-kai da suka sace a kauyen.
Wani shugaban al’umma a yankin ya tabbatar da sabon harin ta wayar tarho a ranar Laraba, inda ya ce ’yan bindiga sun sake kai hari a daren Talata da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
Ya ce maharan sun yi garkuwa da Babban Limami da jagoran Fulani tare da wata mata.
Majiyar ta ƙara da cewa ’yan bindigar, waɗanda suka isa da yawa dauke da bindigogi kirar AK-47, sun fara kutsawa gidan Babban Limamin kafin su wuce gidan jagoran Fulanin.
Harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici, inda mazauna da dama suka tsere.
“Ko a yanzu da nake magana da kai yanzu, mutane da dama sun tsere zuwa garin Kagarko, yayin da wasu ke Sabon-Wuse suna tare da ’yan uwansu,” in ji shi.
Jagoran al’ummar ya nuna takaici kan hare-haren da ke ta aukuwa, yana mai cewa ya aika da kiran gaggawa ga jami’an tsaro sau da dama amma ba a samu amsa ba.
“Mutanenmu suna cikin barazana. Mun yi ƙoƙarin tuntubar jami’an tsaro a Kagarko kan hare-haren da ake kai wa mutanenmu sama da mako guda yanzu, amma babu wani abu da aka yi,” in ji shi.
Wata majiyar ma daga Masarautar Kagarko, wadda ta nemi a boye sunanta saboda dalilan tsaro, ta kuma tabbatar da hare-haren.
Ta ce fadar masarauta ta riga ta kai rahoton lamarin ga Hukumar Karamar Hukumar Kagarko, tare da nuna rashin daukar matakin tsaro.
“Abin takaici ne cewa sama da mako guda, al’ummomi da dama a ƙarƙashin Kagarko suna cikin barazana, amma jami’an tsaro ba sa amsawa duk da kiran gaggawa,” in ji majiyar.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ’yan gudun hijira daga Kohoto da Janjala suna samun mafaka a fadar masarautar.
Fadar ta ce tun da aka kai rahoton lamarin ga hukumar ƙaramar hukuma, ana sa ran jami’an tsaro za su tura dakarun da za su bi ’yan bindiga tare da dawo da zaman lafiya a al’ummomin da abin ya shafa.