Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160
[ad_1]
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, domin tattauna harin ta’addanci da ya faru a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta jihar.
Taron ya gudana ne a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Alhamis, bayan wasu ’yan bindiga sun kai wa ƙauyen Woro hari.
- Ana Fargabar An Kashe Sama Da Mutum 200 A Harin Kwara
- Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Titi Mai Tsawon Kilomita 35 Da Ya Haɗa Al’ummomi 76 A Kaduna
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe mutanen ƙauyen da suka ƙi amincewa da ra’ayoyinsu.
Da farko an ce mutane kusan 75 ne suka mutu, amma sabbin bayanai sun nuna cewa adadin ya ƙaru zuwa kusan mutane 162.
Gwamna AbdulRazaq ya ziyarci yankunan da abin ya shafa ranar Laraba tare da jami’an tsaro.
Ya yi Allah-wadai da harin, sannan ya umarci hukumar kula da agajin gaggawa ta jihar da ta bai wa waɗanda abin ya shafa abinci, matsuguni da sauran kayayyakin tallafi.
A martaninsa, Shugaba Tinubu ya amince da tura bataliyar sojoji zuwa Kaiama.
Haka kuma ya sanar da ƙaddamar da wani sabon atisayen dakarun soji mai suna “Operation Savannah Shield”, domin kawar da ’yan ta’adda da kuma kare al’umma.
Shugaban Ƙasa ya yi Allah-wadai da harin, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta tsaro a yankin.
[ad_2]
Source link