’Yan bindiga sun kashe mutum 10 a ƙauyen Kwara
[ad_1]
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu bayan ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara.
Mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun kai harin da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Talata.
Mazauna ƙauyen sun ce adadin ’yan bindigar da suka kai harin ya kai mutum 200, kuma sun shiga ƙauyen suna harbe-harbe.
Wani mazaunin yankin, Ahmed Yinusa, ya ce maharan sun shafe sama da awa guda suna cin karensu ba babbaka.
Ya bayyana cewa ƙauyen yana da nisan kilomita 50 daga Kaiama, kuma rashin kyawun hanya ya hana jami’an tsaro isa da wuri.
“‘Yan bindigar suna da yawa, kuma sun kashe mutane da dama. An tabbatar da mutuwar mutane kusan 10, sannan sun ƙone gidaje da dama,” in ji shi.
Wani mazaunin Kaiama, Idris Mohammed, ya ce an kai gawarwaki shida zuwa fadar Sarkin Woro, Alhaji Saliu Bio Umar.
Ɗan majalisar dokokin Jihar Kwara mai wakiltar Kaiama, Halidu Danbaba, ya tabbatar da faruwar harin.
Ya yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su aike ƙarin dakarun soji zuwa yankin Kaiama, musamman ganin makarantu sun fara aiki.
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi Allah-wadai da harin.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rafiu Ajakaye, ya fitar, gwamnan ya ce harin wata alama ce ta nuna cewa ’yan ta’adda na cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren da jami’an tsaro ke kai musu.
Ya ƙara da cewa maharan na ƙoƙarin karkatar da hankalin jami’an tsaro ne bayan nasarorin da aka samu kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link