Wike Ba Matsala Ba Ne Ga APC – Yilwatda
[ad_1]
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce tsohon gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ba matsala ba ne ga jam’iyyar.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Talata, Yilwatda ya bayyana cewa saɓanin da ke tsakanin Wike da gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ba batun APC ba ne, domin Wike ɗan jam’iyyar PDP ne.
- Kotu Ta Yanke Wa Ɗan Fashi Hukuncin Kisa A Nasarawa
- EFCC Ta Kama Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, Bisa Zargin Wulaƙanta Takardun Naira
Ya ce batun yunƙurin tsige gwamnan da ke faruwa a Jihar Ribas ya shafi ’yan majalisar dokokin jihar na APC ne kaɗai, kuma lamari ne na cikin gida.
Yilwatda ya ƙara da cewa APC na da hanyoyin da take bi wajen warware matsalolin cikin gida.
Hakazalika, ya dace a riƙa magance irin waɗannan batutuwa cikin natsuwa.
Ya jaddada cewa Wike ba shi da wata matsala da APC.
[ad_2]
Source link