Kotun Bauchi ta yanke wa barawon babur hukuncin kisa ta hanyar rataya
[ad_1]
Babban Kotun Jihar Bauchi mai lamba hudu, ta yanke wa wani mutum mai suna Mamuda Zakariyau hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin kashe wani mai babur da wuƙa a lokacin da ya yi yunƙurin satar babur ɗin.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Aliyu Baba Usman, ya ce: “Saboda kotu ta same ka da aikata laifin kisan kai, wanda hukuncinsa kisa ne, an yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya.”
Lauyoyin Ma’aikatar Shari’a sun gabatar da tuhuma guda biyu a kan Mamuda, inda suka ce a ranar 16 ga watan Oktoba, 2026, Mamuda ya haɗa baki da wani Sadiq, wanda aka fi sani da Gwaska (wanda ake nema a yanzu), suka hau babur ɗin Basiru Mohammed.
Lauyan ya ce mutanen sun nemi ya kai su tsohon filin jirgin sama, amma sai suka daba masa wuƙa suka kwace babur ɗin.
Laifin, a cewar lauyan ya saba wa sashe na 1(2) na dokar fashi da makami (LFN 2004).
Kazalika, lauyoyi sun tuhumi Mamuda da abokinsa da yin kisan kai ta hanyar daba wa Basiru wuƙa, wanda ya fadi ya mutu a nan take, wanda shi kuma laifin ya saba wa sashe na 217 na dokar Penal Code ta Bauchi.
Mai gabatar da ƙara ya kira shaidu hudu, ya kuma gabatar da shaidu biyar da suka haɗa da wayar hannu, babur, wuƙa mai dauke da jini da kuma takalma.
Lauyan wanda ake ƙara, Barista Kayode Omosehin, ya nemi kotu ta wanke Mamuda, yana mai cewa babu shaidun ido da suka tabbatar da aikata laifin, kuma tuhumar ta saba wa tsarin shari’a.
Sai dai a hukuncinsa, Mai Shari’a Aliyu Baba Usman ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da dukkan tuhume-tuhumen, inda aka same shi da laifin fashi da makami da kuma kisan kai, wanda hukuncinsa kisa ne.
A watan Oktoban 2025, rundunar ’yan sandan Bauchi ta kama Mamuda Zakariyau mai shekaru 30 bisa zargin daba wa mai babur wuƙa har lahira da kuma satar babur ɗinsa.
An ce Mamuda ya daba wa Mohammed Basiru wuƙa, wanda ya fadi ya mutu, sannan ya tafi da babur ɗinsa kirar Bajaj Boxer ja mai lambar NNG 813 UM.
Kafin mutuwar Basiru, ya yi kururuwar da ta jawo hankalin mazauna yankin.
Bayanai sun nuna mutane sun bi Mamuda, lamarin da ya tilasta masa barin babur ɗin ya gudu.
Daga bisani ’yan sanda sun isa wurin, suka garzaya da Basiru zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Daga baya an gano Mamuda ta hanyar bayanan da aka samu daga wayarsa, aka kuma kama shi.
A lokacin tambayoyi, Mamuda ya amsa laifin, yana mai cewa ya aikata ne saboda buƙatar kuɗi don ya auri mata ta uku.
Ya amince cewa ya yaudari mai babur kafin ya daba masa wuƙa ya kwace babur ɗinsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link