EFCC Ta Kama Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, Bisa Zargin Wulaƙanta Takardun Naira

[ad_1]

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC), reshen jihar Kano, ta kama wata fitacciyar jarumar Kannywood kuma ‘yar TikTok, Samha Inuwa, a ranar Talata, 3 ga Fabrairu, 2026, bisa zargin wulaƙanta takardun kuɗin Naira.

An kama Samha ne bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda aka hango ta tana share majina daga hancinta da takardun kuɗin Naira a fili, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

  • An Fitar Da Sakon Bidiyo Na Yayata Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Tunisia
  • NDLEA Na Neman Al’umma Ta Goyi Bayan Shirye-shiryenta Na Yaƙi Da Noman Wiwi

Bayan bayyanar bidiyon, EFCC ta ce ta ɗauki matakin gaggawa, inda ta bi sahun gano inda take tare da kama ta domin amsa tambayoyi dangane da zargin.

A halin yanzu, Samha na tsare a ofishin hukumar yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a kanta.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken da ake yi a kan lamarin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *