Matashi ya daddatsa mahaifinsa da adda har lahira
[ad_1]
Wani matashi ya shiga hannun hukuma kan zargin sa da kashe mahaifinsa ta hanyar daddatsa shi da adda a Jihar Kuros Riba.
Ana zargin Bassey Ubi, ya yi wa mahaifinsa kisan gilla ne bayan sun sanu saɓani a ranar Asabar.
Washegari bayan kowannensu ya dawo daga coci cacar baki ta kaure tsakaninsu a gidan nasu da ke unguwar kusa da fadar basaraken O-3 , Usaja, da ke Ikpakapit Abgarun Ugep, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Yakurr, Jihar Kuros Riba.
Kisan gillar da ɗan ya yi wa mahaifinsa ya yi matuƙar harzuƙa matasan unguwar inda su ma suka yi kukan kura suka kama shi, za su ɗauki mataki a kansa, kafin ’yan sanda ƙwace shi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba, ASP Sunday Eitokpah, ya tabbatar wa da Aminiya cewa wanda ake zargin yana hannu, ana yi masa bincike da, zarar an gama za a miƙa shi a kotu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link