An Kaddamar Da Layin Dogo Mai Kwarin Daukar Nauyi Na Farko A Hamada A Afirka Da Kamfanin Sin Ya Gina
[ad_1]
An kaddamar da layin dogo mai kwarin daukar nauyi na farko a hamada a yankin Afirka, watau layin dogo da ke kan layin hakar ma’adanai na yammacin kasar Aljeriya a hukumance, a ranar 1 ga watan nan. Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya sanar da fara aikin layin dogon a hukumance yayin bikin budewa.
Layin dogon da ke kan layin hakar ma’adanan yana da jimillar tsawon kilomita 950, wanda daga ciki kilomita 575 kamfanin gina layin dogo na kasar Sin da kuma kamfanonin cikin gida na kasar ta Aljeriya ne suka gina, inda hakan ya sanya shi zama babban aikin samar da ababen more rayuwa da kamfanonin Sin suka gudanar a Aljeriya. Bayan fara amfani da layin dogon, zai kara inganta hanyoyin sufuri na layin dogo a kasar ta Aljeriya, da kuma taimakawa wajen sada lardunan kudu maso yammacin Aljeriya da kuma habaka tattalin arzikinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link